Garambawul: Gwamna Ya Rantsar da Kwamishinoni 6, Ya Kirkiro sababbin Ma’aikatu
- Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya yi sauye sauye a majalisar jiharsa yayin da ya sanar da kirkirar wasu sababbin ma'aikatu shida
- Wannan na zuwa ne yayin da Otti ya rantsar da sababbin kwamishinoni shida a ranar Laraba a kokarin cika gibin mukarrabansa
- A yayin garambawul din, an rasa daga cikin kwamishinonin an sauya masu ma'aikatu, sai dai ma'aikatar noma ba ta samu kwamishina ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abia - A ranar Laraba, Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya rantsar da kwamishinoni shida a wani yunkuri na yiwa majalisarsa garambawul.
Kwamishinonin sun karbi rantsuwar kama aiki daga babban lauyan gwamnati kuma sakataren dindindin na ma'aikatar sharia'a na jihar.
Mai magana da yawun gwamnan, Ukoha Njoku ya fitar da sanarwa a ranar Laraba wacce ke dauke da bayanai kan rantsuwar inji rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sababbin kwamishinonin da aka ranstar
Sababbin kwamishinonin da aka rantsar sun hada da David Kalu, Kingsley Nwokocha, Uwaoma Ukandu, Ijeoma Aghkwa, Goodluck Ubochi da Ogbonnaya Uche, farfesa.
Da yake jawabi a wurin bikin, Gwamna Otti ya shaida wa sababbin kwamishinonin cewa:
"Aikin gudanar da harkokin gwamnati babban aiki ne wanda ke bukatar samun mutanen da suka kware a tafiyar da ma'aikatu domin ganin gwamnati ta cimma manufofinta."
Da take mayar da martani a madadin abokan aikinta, Misis Agukwa daya daga cikin sababbin kwamishinonin ta bayyana nadin nasu a matsayin wata dama ta yiwa Abia aiki.
Gwamna ya yi wa majalisarsa garambawul
Hakazalika, Gwamna Otti ya sanar da sunayen ma'aikatun da sababbin kwamishinonin shida za su jagoranta a ranar Alhamis, kamar yadda wata sanarwar Mista Njoku ta nuna.
Gwamnan ya kuma sanar da yin sauye-sauye a majalisar mukarrabansa da kuma kafa sababbin ma'aikatu.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gwamnan ya kirkiro sababbin ma’aikatu guda shida da suka hada da ma'aikatar ilimin firamare da sakandare da ta ilimin manyan makarantu.
Sauran sun hada da ma'aikatar yaki da talauci da bunkasa al'umma; kwadago da ayyuka; masana'antu, kasuwanci da kirkira da kuma al'adu da tattalin arziki.
A yayin garambawul din, an ruwaito cewa wasu daga cikin kwamishinonin an sauya masu ma'aikatu yayin da ma'aikatar noma ba ta samu kwamishina ba.
Gwamna Makinde ya yi sauye sauye
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ya yi wani dan karamin garambawul a majalisar zartaswan jiharsa.
Gwamnan ya sauyawa wasu kwamishinoni wuraren aiki domin inganta ayyukan gwamnatinsa da kuma ƙoƙarin cika muradan al'ummar Oyo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng