Mutane 39 Sun Kamu da Cutar Kyandar Biri a Najeriya, NCDC Ta Dauki Matakan Gaggawa
- An samu bullar cutar kyandar biri a wasu jihohin Najeriya yayin da hukumar NCDC ta ce mutane 39 ne suka kamu a halin yanzu
- Hukumar NCDC mai ke dakile yaduwar cututtuka a Najeriya ta ayyana kyandar biri matsayin cutar da ke bukatar daukar matakin gaggawa
- NCDC ta bayyana matakan da gwamnati ta dauka domin dakile yaduwar cutar da kuma lissafa jihohin da cutar ta fi bulla a fadin kasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce mutane 39 sun kamu da cutar kyandar biri a fadin jihohi 33 da kuma babban birnin tarayya.
Shugaban NCDC, Dakta Jide Idris, ya bayyana hakan a lokacin da ya ayyana cutar kyandar biri a matsayin cutar da ke bukatar daukan matakin gaggawa kanta a duniya.
Jihohin da kyandar biri ta fi bulla
A wani taron manema labarai a jiya Alhamis, Channels TV ta rahoto NCDC ta ce ta kara sanya ido a fadin Najeriya domin ganowa da kuma daukar mataki a inda aka ji cutar ta bulla.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakta Jide ya lissafa wasu daga cikin jihohin da kyandar biri ta bulla a kasar da suka hada da: Bayelsa (mutum 5), Cross River (mutum 5), Ogun (mutum 4) da Legas (mutum 4).
Sauran jihohin da cutar ta bulla sun hada da: Ondo (mutum 3), da Ebonyi (mutum 3), wadanda NCDC ta ce su ne suka sami mafi yawan bullar cutar.
NCDC ta dauki matakai kan kyandar biri
Cibiyar NCDC ta ce zuwa yanzu an tsaurara sa ido a wasu jihohi da suka hada da Legas, Enugu, Kano, Ribas, Cross-River, Akwa-Ibom, Adamawa, Taraba da Abuja.
"Kwamitin ma'aikatan da ke sa ido kan kyandar biri ta ƙasa (TWG), kwamiti ne da aka kirkira karkashin NCDC domin ci gaba da sanya ido da kuma tattara rahoto kan cutar.
“A wani bangare na kokarin da gwamnati ke yi, mun kara sanya ido a duk fadin Najeriya domin ganowa da kuma mayar da martani a duk inda aka samu bullar cutar.
NCDC na jiran rigakafin kyandar biri
Hukumar ta NCDC ta ce tana duba yiwuwar yin allurar rigakafi ga yankunan da suka fi fuskantar hatsarin kamu da cutar, in ji rahoton The Cable.
"Najeriya na sa ran samun allurai 10,000 na rigakafin Jynneos".
- A cewar shugaban NCDC.
Hukumar NCDC ta sanar da asibitocin gwamnati da masu zaman kansu game da barkewar kyandar biri tare da aika wadanda suka kamu zuwa cibiyoyin kulawa a da ke a shiyyoyi 6 na fadin kasar.
"Kyandar biri ta bulla a Afrika" - WHO
A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta ayyana barkewar cutar kyandar biri a wasu kasashen Afrika da suka hada da Jamhuriyyar Congo.
Hukumar ta ce akwai damuwa sosai kan bullar sabon nau'in cutar da kuma saurin yaduwarta a gabashin Congo da makotanta wanda ke zama barazana ga lafiya a duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng