Muhimman abubuwan da ya dace ku sani game da cutar ƙyandar biri

Muhimman abubuwan da ya dace ku sani game da cutar ƙyandar biri

  • Annobar da ta kunno kai a duniya a wannan lokacin ita ce cutar kyandar biri, ana iya kamuwa da cutar Kyandar Biri tsakanin kwanaki 6 zuwa 13 amma ta kan canza daga 5 zuwa kwanaki 21 a cewar WHO
  • Alamomin cutar sun hada da zazzabi, ciwon kai, radadin jiki, rashin kuzari, ciwon makogoro, kaluluwa a wuya da dasashi, bayan nan sai bayyanar kuraje a fuska, tafukan hannu, tafin kafa, al'ura da sauransu
  • Cibiyar hana yaduwar cutuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa, har yanzu ba a ji wanda cutar ta halaka ko illata ba, amma ta fi tsananta ga kananan yara, mata masu juna biyu ko mutanen dake da matsalar garkuwar jiki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Kyandar Biri

Cutar na iya yaduwa ta hanyar mu'amala da mai dauke da cutar, gumi, yawu da abubuwan da mai cutar yake amfani dasu kamar makwanci, a cewar Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO).

Kara karanta wannan

Sabuwar ɓaraka ta kunno kai a APC, mambobin NWC 2 sun buƙaci a yi wa Sanata Adamu ta-waye

Hukumar kiwon lafiyar ta duniya ta kara da bayyana cewa lokacin bayyanar cutar kyandar biri tsakanin kwanaki shida zuwa 13 ne amma zai iya zama tsakanin kwanaki 5 zuwa 21.

Muhimman abubuwan da ya dace ku sani game da cutar ƙyandar biri
Muhimman abubuwan da ya dace ku sani game da cutar ƙyandar biri. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika, hukumar ta ce kyandar biri ba ta cika illata mutum ba, amma za ta iya yin kamari ga wasu, kamar yara, mata masu juna biyu ko mutanen dake fama da matsalar garkuwar jiki saboda wasu cutuka daban.

Alamomin cutar

Kamar yadda Cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana, alamomin cutar sun hada da bayyanar zazzabi, ciwon kai, radadin jiki, rashin kuzari, ciwon makogoro, kaluluwa a wuya da dasashi, daga bisani kuraje su bayyana (yawancin lokuta masu karfi ko su duri ruwa) a fuska, tafin hannu, tafin kafa, al'ura da sauran sassan jiki.

Yadda za a iya kare kai daga kamuwa da cutar

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: EFCC ta sake bankado wata badakalar biliyan N90 kan Akanta-Janar, ya zama biliyan N170

NCDC ta bayyana wasu matakai da ya kamata al'umma ta bi don gudun kamuwa da cutar.

NCDC ta bukaci jama'a da su farga da hatsarin kamuwa da Kyandar Biri sannan su kiyaye dokokin tsare kawunansu ta hanyar bin dokoki da ka'ida.

Ya kamata jami'an kiwon lafiya su sa ido idan sun zargin wani da kamuwa da Kyandar Biri sannan su sanar ga kungiyar kula da cutar fata ta jihar don ta lura da lamarin tare da yin gwajin cutar.

Har ila yau, cibiyar ta shawarci duk wanda ya ga alamomin cutar da ya garzaya asibiti mafi kusa.

Kamar yadda cibiyar ta bayyana, duk da hatsarin kamuwa da Kyandar Biri a Najeriya ya tsananta bisa binciken da NCDC tayi cikin kwanakin nan, a halin yanzu a kasar da duniya baki daya an gano cewa babu wani barazana ga rayuwa ko al'umma wanda zai zamo sanadiyyar tsananta cutar ko yaduwar cutar cikin sauri.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Amma cibiyar za ta cigaba da lura da lamarin tare da sanar wa jama'a matakan da ya kamata su bi don tsare lafiyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel