"Babu Amfanin Tsarin da ba zai Samarwa Talaka Abinci ba," Sheikh Guruntum ga Jagorori
- Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya caccaki shugabannin kasar nan
- Ya ce wasu daga cikinsu tun a duniya za su fara ganin abin da su ka shuka game da jagorantar talakawan kasar nan
- Sheikh Guruntum ya jaddada cewa duk wani kudurin gwamnati da ba zai ba wa talakawa damar samun abinci da sauki ba, ba shi da amfani
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi - Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya bayyana makomar shugabannin da ke barin talakawansu cikin yunwa.
A wani faifan bidiyon karatun malamin, Sheikh Guruntum ya ce babu wani amfani tattare da kudirin gwamnati da ba zai saukakawa talakawa samun abinci ba.
A bidiyon da aka wallafa a shafin Izala na X, Shehin malamin ya ce tun a duniya wasu daga cikin jagorori za su fara ganin sauyin rayuwa kafin a je gaban Allah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce da yawa daga cikin wadanda Allah ya ba mulki ba su san ta yaya za su jagoranci jama'ar kasar nan yadda ya dace ba.
"Shugabanni abin tausayi ne," Sheikh Guruntum
Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum ya ce shugabanni, musamman wadanda ba su sauke nauyi abin tausayi ne.
Ya ce wasu daga cikin jagororin ba su ma san menene shugabancin ba, sai an je gaban Allah SWT ido zai raina fata, bayan an fara lissafa masu abubuwan da su ka ki yi.
Sheikh Guruntum ya kara da cewa ana samun rafkanuwa a cikin shugabanci, wanda ke sanya jagorori manta nauyin jama'a da su ke dauke da shi.
Sheikh Guruntum ya nusar da matasa
A baya mun kawo labarin yadda sanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi wa masu bin shafukan batsa wa'azin su shiga hankalinsu.
Sheikh Guruntum ya ce Allah SWT ya na fushi da masu yada hotuna da bidiyo ko sakonnin batsa a kafafen zamani, kuma Allah zai iya jarabtar mai halin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng