Tsarin Tinubu Ya Jefa Jami’o’i a Matsala, Za a Ƙarawa Dalibai N80,000 a Kudin Makaranta

Tsarin Tinubu Ya Jefa Jami’o’i a Matsala, Za a Ƙarawa Dalibai N80,000 a Kudin Makaranta

  • Kungiyar malaman jami'a ta kasa ta koka kan karin kuɗin wuta da gwamnatin Bola Tinubu ta yi sakamakon cire tallafin lantarki
  • ASUU ta yi magana kan yadda kuɗin wuta ya karu da kashi 300% a kusan dukkan jami'o'in Najeriya musamman wanda suke sahun farko
  • Kungiyar ASUU ta fara maganar ƙarin kuɗin wuta ga daliban da suke karatu a jami'o'i domin samun biyan kudin wutar lantarki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU ta fitar da sanarwa kan karin kuɗin wuta da gwamnatin tarayya ta yi.

ASUU ta ce cire tallafin lantarki da karin da aka yi wa yan layin Band A ya kara yawan kuɗin wuta da jami'o'i ke biya.

Kara karanta wannan

Dattijon Arewa ya jaddadawa Tinubu matsayarsa, Yakasai ya fadi matsalar Najeriya

Daliban jami'a
Ana shirin kara kudin lantarki a jami'o'i. Hoto: Frederic Soltan
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kungiyar ASUU ta ce za ta duba yiwuwar fito da biyan kudin wuta ga daliban jami'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya jawo karin kudin wutan jami'o'i

Kungiyar ASUU ta ce kafin cire tallafin lantarki dukkan jami'o'in Najeriya suna biyan Naira biliyan 5 ne ko abin da ya yi kama da haka a duk wata.

Amma a cewar shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke bayan karin kudin wutar a yanzu haka suna biyan sama da Naira biliyan 21.

Watakila ayi wa daliban jami'a karin N80,000

Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce sun tura takarda ga gwamnatin tarayya kan neman ƙirƙiro sabon tsarin biyan kudin lantarki a jami'o'i.

Emmanuel Osodeke ya ce ASUU na hasashen cewa kowane dalibi zai rika biyan N80,000 a matsayin kudin shan wutar lantarki.

Za a bambance jami'o'i a kudin lantarki

Kara karanta wannan

Jigawa: Wasu matasa 2 sun mutu a yanayi mai ban tausayi a hanyar zuwa Kasuwa

Sai dai a wani bayani da Farfesa Emmanuel Osodeke ya yi ya ce za a lura da tsarin da jami'a take kai wajen biyan kudin da za a kara.

Jaridar Leadership ta wallafa cewa za a rika lura da jami'o'i da suke layin Band A da sauransu wajen karin kudin.

JAMB ta karrama wasu jamio'in Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar jarrabawar JAMB ta kaddamar da taron karrama jami'o'i da suka yi zarrra a Najeriya kan daukar dalibai ta hanyar da ta dace.

A wannan karon, jami'o'i uku daga Arewacin Najeriya ne suka lashe dukkan kyaututtuka da lambar yabo da hukumar JAMB ta bayar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng