Minista Ya Fadi Miliyoyin Alburusan da Jami'an Tsaro ke Bukata Duk Shekara

Minista Ya Fadi Miliyoyin Alburusan da Jami'an Tsaro ke Bukata Duk Shekara

  • Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa jami'an tsaron kasar nan na bukatar alburusai da dama domin yakar ta'addanci
  • Ministan ya ce ana bukatar akalla alburusai miliyan 350 domin rabawa dakarun sojoji, 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a kowace shekara
  • Ya bayyana haka ne jim kadan bauan ma'aikatar tsaro ta rattaba hannu a kan wata yarjejeniya da wasu hukumomi domin samar da makamai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar nan na bukatar akalla alburusai miliyan 350 domin gudanar da ayyukansu duk shekara.

Karamin Minisan tsaro, Bello Matawalle ne ya sanar da haka a babban birnin tarayya Abuja, jim kadan bayan sanya hannu a kan yarjejeniya da wasu hukumomin kasar nan biyu.

Kara karanta wannan

Dattijon Arewa ya jaddadawa Tinubu matsayarsa, Yakasai ya fadi matsalar Najeriya

Dr. Bello Matawalle
Ministan tsaro ya ce jami'ai na bukatar alburusai miliyan 350 don yaki da rashin tsaro Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta bayyana cewa hukumomin tsaron da su ka kulla yarjejeniyar sun hada da Defence Indutries Corporations of Nigeria (DICON), da hukumar kimiyya da aikin injiniya ta kasa (NASENI).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhimmancin samar da makamai a tsaro

Karamin ministan na tsaro ya bayyana muhimmancin samarwa jami'an tsaron nan kasar nan, tare da kera makaman da jami'an za su bukata a cikin kasar nan domin inganta tsaro.

Bello Matawalle ya bayyana haka ne bayan sanya hannu kan yarjejenyar samar da wurin hada makamai a Abuja, da hadin gwiwar DICON da NASENI.

Manyan jami'an soja ne su ka halarci taron, ciki har da babban hafsan sojojin kasar nan, Janar Christopher Musa da shugabannin tsaron kasar nan, da na sauran hukumomin tsaro.

Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro

A wani labarin kun ji cewa majalisar wakilai ta kasa ta bi umarnin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu inda ta gayyaci jami'an tsaro da sauran shugabanni a bangaren tsaro.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta kawo shawarar yadda za a cafke barayin man fetur

An gayyaci jagororin tsaron bisa umarnin shugaban kaa, Bola Ahmed Tinubu, kuma ana sa ran za su yiwa majalisar cikakkaen bayanin kan umarnin da Tinubu ya ba su na su koma noma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.