Gwamnati Ta Jero Sharudan Shigo da Abinci daga Waje ba tare da Biyan Haraji ba

Gwamnati Ta Jero Sharudan Shigo da Abinci daga Waje ba tare da Biyan Haraji ba

  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fitar da ka'idojin da sai masu shigo da kayan abinci sun cika kafin su shigo da abinci mara haraji
  • Tun a baya gwamnatin tarayya ta ce ta dakatar da haraji a kan wasu kayan abinci da ake shigowa da su domin saukaka farashinsu
  • Daga cikin ka'idojin da aka gindaya akwai tabbatar da biyan haraji na shekaru biyar da mika takardun bayanan kudin kamfanoni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Bayan ɗaukar alkawarin samar da matakan sauƙaƙa farashin abinci a kasa, gwamnatin tarayya ta fitar da sharuɗɗan shigo da kayan abinci ba tare da haraji ba.

Kara karanta wannan

Babu haraji: Bayani dalla dalla kan sharuddan shigo da abinci Najeriya kyauta

Gwamnatin na ganin wannan mataki zai rage raɗaɗin da yan ƙasa su ke ciki na tsadar kayan abinci, kuma ya fara aiki daga watan Yuli zuwa Disamba 2024.

Tinubu
Gwamnati ta fitar da matakan shigo da abinci mara haraji Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta tattara cewa gwamnatin ta zabi wasu abinci da ta ke ganin su 'yan Najeriya su ka fi amfani da su, sannan ta janye harajin shigo da su da harajin VAT.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharuddan shigo da abinci mara haraji

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ma'aikatar kuɗi ta gindaya wasu sharuɗɗan da sai mai kamfani ya cika kafin ya shigo da abinci ba tare da biyan haraji ba.

Jaridar Punch ta wallafa cewa daga cikin sharuɗɗan da hukumar kwastam ta ƙasa ta bayyana akwai:

1. Mika takardun bayanan kudi

Hukumar kwastam ta bayyana cewa dole sai mai shigo da kaya ya bayar da bayanan takardun kudin kamfaninsa.

Kara karanta wannan

Kudin da kowane gwamna ya tashi da su da Tinubu ya raba Naira biliyan 430 a jihohi 34

Sauran bayanan sun hada da kuɗin da kamfani ke samu a duk shekara, shaidar biyan haraji da kuma albashin da ake biya na shekaru biyar.

2. Mallakar wurin casar shinkafa

Ga waɗanda za su shigo da ɗanyar shinkafa, dawa da masara daga sharaɗin da dole sai sun cika akwai mallakar wurin casa shinkafa.

Dole sai wurin casa shinkafar zai iya gyara shinkafa tan 100 a rana, kuma sai ya shekara huɗu ya na aiki.

Hukumar kwastam ta ce ma'aikatar kuɗi za ta riƙa ba ta bayanan masu shigo da abincin da adadin da aka amince su shigo da shi lokaci zuwa lokaci.

Gwamnati ta fadi lokacin shigo da abinci

A baya kun ji cewa gwamnatin ƙasar nan ta bayyana shirinta na fara shigo da abinci mara haraji, a wani mataki na rage hauhawar farashi a ƙasar.

Shugaban hukumar kwatsam na kasa, Bashir Adeniyi ne ya bayyana cewa shirin zai fara aiki a makon nan, tare da bayyana fatan shirin zai cimma manufarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.