'Yan Daba Sun Sace Takardun Shari’ar Ganduje a Kotu Lokacin Zanga Zanga a Kano
- Gwamnatin Kano ta yi bayani kan yadda yan daba suka sace takardun da ake shari'ar shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje
- Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar gani da ido ma'ikatar shari'ar jihar Kano bayan kammala zanga zanga
- Gwamnatin jihar ta yi zargin cewa an dauko yan daba ne zuwa Kano domin su tayar da tarzoma a lokacin zanga zangar tsadar rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta yi bayani kan shari'ar zargin rashawa da ake yiwa shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje.
Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa an sace takardun da ake tattara bayanan shari'ar Abdullahi Ganduje da gwamnatin Kano.
Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya wallafa bayanin gwamnan a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shari'ar Ganduje da gwamnatin Kano
Tun bayan hawan Abba Kabir Yusuf gwamna ya zargi Abdullahi Ganduje da wawushe kudi a jihar.
Hakan ya sa aka fara shari'a tsakanin gwamnatin Kano da Ganduje domin tabbatar da mai gaskiya a tsakaninsu.
An sace takardun shari'ar Ganduje
A lokacin da aka fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya, wasu mutane su kai hari ma'aikatar shari'a a Kano.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa a cikin barnar da aka yi a lokacin an sace takardun da ake rubuta bayanan shari'ar Ganduje.
Wanene sace takardun shari'ar Ganduje?
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zargi yan daba da suka kai hari ma'aikatar shari'a da sace takardun.
Abba Yusuf ya ce an dauko hayar yan dabar ne na musamman domin su sace takardun a cikin kotun.
Gwamnan ya ce an yi hakan ne domin a kubutar da Ganduje, iyalansa da sauran jami'an gwamnatinsa daga zargin wawushe kudin da ake musu.
Muaz Magaji ya yi maganar 'badakalar' Goggo
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon kwamishinan ayyukan Kano, Muaz Magaji ya yi magana kan zargin Hafsat Abdullahi Ganduje da wawushe kudin Kano.
Mai bidiyon barkwanci, Dan Bello ne ya zargi Hajiya Hafsat Abdullahi Ganduje da wawushe kudin Kano har Naira biliyan 20.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng