Majalisar Tarayya Ta Janye Kudirin Daure Marasa Rera Taken Najeriya a Gidan Yari

Majalisar Tarayya Ta Janye Kudirin Daure Marasa Rera Taken Najeriya a Gidan Yari

  • Majalisar wakilai ta dakatar da sabon kudurin da aka bijiro da shi domin hukunta wadanda ba sa rera taken Najeriya
  • Haka kuma kudurin ya kunshi dokar dauri ga masu lalata alamomin kasar nan da wuraren ibada gabanin janye ta
  • Shugaban majalisa, Tajuddeen Abbas ya bayyana janye kudurin a zaman majalisa na yau Laraba bayan surutun jama'a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT , Abuja - Majalisar wakilai ta kasa ta bayyana cewa an janye kudurin dokar da za ta hukunta yan Najeriya da su yi wasarere da rera taken kasa ko makamantan laifuka.

Daga cikin tanade-tanaden kudirin , akwai hukunta masu wulakanta alamomin kasar nan da kuma lalata wurin ibada a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta kawo shawarar yadda za a cafke barayin man fetur

Majalisa
Majalisa ta janye dokar hukunta yan Najeriya marasa rere taken kasa Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Kudirin kare taken Najeriya ya bar Majalisa

Majalisar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa shugaban majalisar da kansa ne ya bijiro da kudurin a ranar Talata , 23 Yuli, 2024, kuma tuni ya jawo Allah wadai daga jama'ar kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta ce shugabanta ya zurfafa bincike domin gano ko kudurin zai yi dai-dai da cigaban yan kasar nan domin tabbatar da nasarar bunkasa Najeriya.

Majalisar Wakilai ta fadi dalilin janye kudurin

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kasar nan ta bayyana dalilan janye dokar hukunta masu wulakanta taken kasar nan da dangoginsa, da lalata wuraren ibada.

Majalisar ta bayyana cewa shugabanta, Rt.Hon. Tajuddeen Abbas mai jin koken 'yan kasar nan ne, kuma ba zai yi abin da zai takurawa kowa ba, musamman bayan shawarwari.

Mashawarcin shugaban majalisa, Musa Krishi ya ce Rt. Hon. Abbas ya tattauna da kusoshin kasar nan kuma ya amince da shawarar dakatar da kudurin dokar.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

Cin hanci: An nemi binciken dan majalisa

A wani labarin mun ruwaito cewa wasu kungiyoyin Arewacin kasar nan sun nemi binciken dan majalisa, Hon. Ugochinyere Ikenga bisa zargin ba wa shugaban majalisa cin hanci.

Kungiyoyin da su ka gana da manema labarai a Kaduna sun jaddada cewa akwai bukatar a duba shaidar da ake da tantamar za ta tabbatar da zargin cin hancin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.