Kamfanin Simintin Dahiru Mangal Ya Yi Magana Kan Siyar da Buhu a N6,000
- Kamfanin simintin Dahiru Mangal ya ƙaryata jita-jitar siyar da siminti kan N6,000 kamar yadda wani ya fada
- Kamfanin ya shawarci al'umma da su guji amincewa da rade-radi idan ba daga kamfanin suka samu bayani ba
- Wannan na zuwa ne bayan wani matashi ya yada a kafar X cewa ya sayi kowane buhun siminti a kan N6,000
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kamfanin siminti na Dahiru Mangal ya fitar da sanarwa kan jita-jitar siyar da siminti kan N6,000.
Kamfanin ya ƙaryata zancen inda ya bukaci al'umma su guje yada jita -jita kan farashin da ake ta yaɗawa.
Kamfanin Mangal ya magantu kan farashin siminti
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a shafin X a jiya Talata 13 ga watan Agustan 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin ya bukaci al'umma su dogara da shafukan watsa labaransu domin samun sahihan labarai domin gujewa fadawa hannun azzalumai.
Har ila yau, kamfanin ya tabbatar da himmatuwarsa wurin samar da kaya mai inganci domin kyautata alaka da abokan hulda.
Kamfanin simintin Mangal ya ba al'umma shawara
"Mun samu wani labari da ke yawo a kafofin sadarwa game da farashin siminti a kamfaninmu."
"Domin samun sahihan labarai, muna shawartarku da ku rika tuntubar masu kula da abokan huldarmu, suna nan a kowane lokaci domin ba ku hadin kai."
"Ku guji amincewa da duk wani farashin da bai zo daga wurinmu ba, muna tabbatar muku da samar da kaya masu inganci, mun gode da yarda da kuka yi da mu."
- Kamfanin Mangal
Kamfanin mai suna Mangal Cement Company mallakar attajirin jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal ne, an kashe kimanin $1.5bn wajen gina shi.
An yada farashin bogin simintin Mangal
Kun ji cewa wani mai amfani da kafar X ya yada yadda ya sayi buhun siminti kan N60,000 a kamfanin Dahiru Mangal da ke jihar Kogi.
Matashin mai suna Maleek Anas shi ya bayyana haka inda mutane ke tambaya yadda za su samu siminti cikin sauki a shaguna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng