Satar Kayan Dakin Ibada Ya Jefa Rayuwar Tela cikin Garari, Kotu Ta Yanke Hukunci

Satar Kayan Dakin Ibada Ya Jefa Rayuwar Tela cikin Garari, Kotu Ta Yanke Hukunci

  • Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.hankali bayan kotun majistare ta yanke masa hukunci
  • Kotun, karkashin Mai Shari'a Shawomi Bokkos ta kama matashi Arron Garba mai shekaru 22 da laifin sata, wanda ya karya dokar kasa
  • Yanzu haka alkalin ya yanke masa hukuncin daurin watanni 18 da zabin biyan tara, sannan zai biya diyyar wata N100,000 da zabin zaman gidan yari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Filato - Kotun majistare da ke zamanta a Jos, babban birnin jihar Filato ta kama wani matashi, Arron Garba da laifin sata, tare da yanke masa hukunci.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta kawo shawarar yadda za a cafke barayin man fetur

Ana zargin Arron mai shekaru 22 da cire tagogin wani coci, kuma ya amsa laifinsa a gaban alkalin kotun, Shawomi Bokko.

Police
Kotu ta daure matashin da ya saci tagogin coci na tsawon watanni 18 Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa Mai Shari'a, Shawomi Bokko ya yanke hukuncin daurin watanni 18 bisa satar tagogin, amma an ba wa matashin zabin ya biya tarar N50, 000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashin barawon taga zai biya diyya

Kotun majistare da ke zamanta a Jos ta umarci matashi Arron Garba da biyan tarar N100,000 bisa sace tagogin wata coci a yankin da ya ke, ko a kara masa wa'adin zaman gidan maza na wata shida.

Mai Shari'a, Shawomi Bokko ne yanke hukuncin bayan hukuncin zaman gidan kaso na watanni 18 ko tara na kama Arron Garba da laifin sata, Jaridar PM News ta wallafa.

An kama kwararren barawon kayan coci

A wani labarin kun ji cewa jami'an tsaron kungiyar So-safe sun yi ram da wani matashi da ake zargin ya kware wurin satar kayan coci a yankin Ado-Odo/Ota, da ke jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

An cafke matashin ne ya na tsaka da kokarin tserewa da kayan sata da ya dauko a wani coci, kuma tuni ya amsa laifinsa tare da bayyana wasu daga cikin cocin da ya yi wa sata a yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.