Gwamna Ya Faɗi Abin da Tinubu Ya Tattauna da Buhari, Shugabanni a Taron Magabata

Gwamna Ya Faɗi Abin da Tinubu Ya Tattauna da Buhari, Shugabanni a Taron Magabata

  • Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da aka tattauna yayin zaman majalisar magabatan kasa
  • Mai girma Nasir Idris ya bayyana cewa an tattauna a kan abubuwan da suka shafi matsalolin da suka jawo zanga zanga a fadin Najeriya
  • Haka zalika gwamnan ya yi karin haske kan batun dawo da tallafin man fetur da yan Najeriya suka buƙaci shugaba Bola Tinubu ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Kebbi ya yi karin haske kan wasu abubuwan da suka shafi kasa bayan zaman majalisar magabatan kasa.

Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa sun tattauna kan wasu abubuwan da suka shafi zanga zangar tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamnati ta tona shirin dan kasar waje na kawo cikas ga mulkin Tinubu

Gwamnan Kebbi
Gwamnan Kebbi ya yi bayani bayan zaman majalisar magabatan kasa. Hoto: Kebbi State Government
Asali: Twitter

Legit ta tattaro bayanan da gwamna Nasir Idris ya yi ne a cikin wata hira da ya yi da tashar DW Hausa kamar yadda suka wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar bukatun masu zanga zanga

Bayan zaman majalisar magabata, gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya bayyana cewa sun duba wasu bukatun masu zanga zanga.

Gwamnan ya ce wasu bukatun da al'umma suka nema suna kan daidai kuma dama aikin gwamnati ne ta saurari koken jama'a.

An fadawa Tinubu ya maido tallafin mai?

Sai dai gwamnan Kebbi ya tabbatar da cewa ba su sanar da shugaban kasa maganar dawo da tallafin man fetur ba a yayin zaman majalisar.

Gwamna Nasir Idris ya ce shugaban kasa ne ya kamata ya duba lamarin tun da dama shi da kansa ya cire tallafin man fetur din.

Maganar barna a lokacin zanga zanga

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

Gwamna Nasir Idris ya nuna takaici kan yadda aka yi kone kone da sace sace a lokacin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Ya bayyana cewa dama wannar ce matsalar da ta sa gwamnati ta yi kira da kaucewa zanga zangar tun a karon farko.

Buhari ya koma Aso Rock a karon farko

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shirya taron majalisar magabata na kasa a fadar shugaban kasa a ranar Talata.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa fadar shugaban kasaa karon farko tun saukarsa a mulkin Najeriya a shekarar 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng