Abubuwan da Suka Wakana a Taron Tinubu da Tsofaffin Shugabannin Najeriya a Aso Rock

Abubuwan da Suka Wakana a Taron Tinubu da Tsofaffin Shugabannin Najeriya a Aso Rock

  • A wajen taron kaddamar da majalisar magabata a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, an tattauna batutuwan da suka shafi kasa baki daya
  • Legit Hausa ta tattaro cewa an gayyaci ministoci bakwai da kuma Nuhu Ribadu, domin yi wa majalisar bayanin halin da kasar ke ciki a yanzu
  • Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya yi magana kan abin da ya faru kafin, a lokacin da kuma bayan zanga-zanga da aka yi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Dele Alake, ministan ma'adanai, ya ce an tattauna batutuwan da suka shafi Najeriya a taron majalisar magabata da aka gudanar a ranar Talata, 13 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Majalisar magabata: Buhari, Jonathan sun magantu kan yadda Tinubu ke mulkin Najeriya

Legit Hausa ta ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ne ya jagoranci zaman majalisar da ya samu halartar Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari, da kuma gwamnonin jihohi 36.

An samu bayanai kan abubuwan da aka tattauna a taron majalisar magabata
Tsoffin shugabannin Najeriya sun ziyarci Aso Rock yayin da Tinubu ya jagoranci taron majalisar magabata. Hoto: @NGRPresident/X
Asali: Facebook

"Majalisar magabata ta godewa 'yan Najeriya" - Alake

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Dele Aleke ne ya yi bayanin abubuwan da suka wakana a taron a yayin ganawa da namena labarai jim kadan bayan fitowa daga taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Alake ya bayyana cewa Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), "ya yi magana kan tsauraran matakan da aka dauka kan tsaro a fadin kasar."

Ministan ya bayyana cewa:

“Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa ya sanar da majalisar magabatan game da abubuwan da suka faru kafin, lokacin da kuma bayan aukuwar zanga-zangar yunwa.
"Ni dai na kira wannan zanga-zangar da wani yunkuri na kifar da gwamnati mai ci, kudurin da bai yiwu ba. Majalisar ta godewa 'yan Najeriya da suka ki yarda da juyin mulki."

Kara karanta wannan

Matasa miliyan 1 za su yi tattakin goyon bayan Tinubu bayan zanga zangar adawa

Majalisar magabata ta yi wa Tinubu addu'a

Shi ma da yake magana, AbdulRahman AbdulRazaq, gwamnan jihar Kwara kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), ya ce majalisar ta tallafawa Shugaba Tinubu da addu’a.

Arise News ta ruwaito AbdulRazaq yana cewa:

"Muna yi masa fatan alheri da addu'ar Allah ya yi riko da hannayensa."

Dubawasu daga cikin jawaban da aka yi a taron a kasa:

Majalisar magabata ta gamsu da Tinubu

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa majalisar magabata ta kasa ta kada kuri’ar gamsuwa da salon mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Majalisar ta bayyana gamsuwarta da sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta bullo da su da kuma “Nasara” da gwamnatinsa ta samu a cikin shekara daya da watanni biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.