An Nemi Makiyaya 11 da Shanu 33 An Rasa a wata Jihar Kudu, Miyetti Allah Ta Koka

An Nemi Makiyaya 11 da Shanu 33 An Rasa a wata Jihar Kudu, Miyetti Allah Ta Koka

  • Rahotanni sun bayyana cewa akalla makiyaya 11 na kungiyar Miyetti Allah ne suka bace tare da shanu 33 a jihar Anambra
  • Kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN ta koka kan yadda ake alakanta 'ya'yanta da ayyukan garkuwa da mutane a jihar
  • MACBAN ta ce 'yan kungiyar sun kasance masu gudanar da ayyukansu bisa doron doka kuma suna neman halaliyarsu a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN ta sanar da batan wasu fulani makiyaya guda 11 da kuma asarar shanu 33 a jihar Anambra.

MACBAN da kungiyar ’yan asalin jihar Anambra (ANIAS) sun musanta ikirarin cewa wasu 'yan bindiga da aka kama a Mgbakwu, da ke Awka ta Arewa, suna da alaka da kungiyoyinsu.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Arewa: 'Yan bindiga sun kashe shugaban makaranta da wasu 6

Miyetti Allah ta yi magana kan makiyaya 11 da shanu da aka nema aka rasa a Anambra
Anambra: Miyetti Allah ta ce an nemi makiyaya 11 da shanu 33 an rasa. Hoto: LUIS TATO
Asali: Getty Images

Kungiyoyin biyu sun yi kira da a gudanar da cikakken bincike a kan zargin satar mutane da ake yi a yankin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MACBAN ta yi magana kan ta'addanci

Sun ce ’yan kungiyar ta MACBAN ba ’yan asalin jihar ba ne amma sun kafa hanyoyin gudanar da rayuwarsu da kuma neman arziki na halal a jihar.

A wata sanarwa da Gidado Siddiki, mataimakin daraktan MACBAN ya fitar, kungiyar ta jaddada cewa tana goyon bayan hukuna duk masu aikata laifuka ba tare da la’akari da kabilarsu ba.

“Ba a iya gane 'yan ta'addan ta amfani da kabilarsu ko inda suka fito ba, mafi akasari neman kudin fansa ke haifar da 'yan ta'addan.
"Mutane da aka kama a wannan yankin ba mu san su ba kuma mai yiwuwa masu sojan gona da fulani makiyaya ne."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Matasa sun aiki gwamna da sako zuwa ga Tinubu, sun zayyana bukatunsu

- A cewar sanarwar Siddiki.

"Makiyaya da shanu sun bata" - Siddiki

Sanarwar ta kuma bukaci hukumomin tsaro da su yi bincike sosai kan matsalar sace-sacen jama’a a jihar tare da tabbatar da cewa wadanda ke da hannu sun fuskanci hukunci.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito Siddiki ya ce an kashe shanu 20 na Haruna Mohammed, sannan kuma shanu 13 na Ibrahim Mohammed sun bace tare da wasu makiyaya 11.

Siddiki ya kara da cewa, saboda tabarbarewar tsaro a farkon wannan shekarar, duk wasu halastattun 'ya'yan kungiyar ta MACBAN sun fice daga yankin.

An kashe shugaban Miyetti Allah

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun hallaka shugaban matasa na kungiyar Miyetti Allah,Yakubu Muhammad a jihar Plateau.

An ce shugaban matasan ya rasa ransa ne a karamar hukumar Bassa da ke jihar a lokacin da 'yan bindigar suka farmake shi da tsakar dare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.