Gwamnatin Tarayya Ta Nunka Albashin Ma’aikatan Shari’a sau 3, Tinubu Ya Sanya Hannu
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kudurin dokar albashi da alawus na ma'aikatan shari'a a matakin tarayya da jihohi
- Shugaban kasar ya rattaba hannu kan dokar da ta karawa ma'aikatan shari'a albashi da kaso 300 kamar yadda hadiminsa, Basheer Lado ya sanar
- Bayan amincewa da kudirin dokar, alkalin alkalan Najeriya, Mai shari’a Olukayode Ariwoola, zai dawo karbar albashin N64m a duk shekara
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan kudirin dokar kara albashi da alawus-alawus na alkalan kasar nan da kashi 300.
Kudurin dokar albashin ma’aikatan shari’ar wanda majalisar dattawa ta amince da shi a watan Yuni, zai bai wa alkalin alkalan Najeriya (CJN) damar samun N64m a duk shekara.
Kudurin karawa alkalai albashi ya zama doka
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata da Basheer Lado, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawa ya fitar a ranar Talata inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Basheer Lado ya sanar da cewa sanya hannun da Tinubu ya yi kan kudirin na nuni da cewa ya nuna “kyakkyawan kudurinsa” na kyautata jin dadin ma’aikatan Najeriya.
Daga cikin fitattun abubuwan da dokar ta kunsa sun hada da, “Tsarin biyan albashi, alawus-alawus, da sauran hakkoki ga ma'aikatan shari’a."
Tinubu ya kyautata albashin ma'aikatan shari'a
Jaridar The Punch ta ruwaito sanarwar da Basheer ya fitar ta ci gaba da cewa:
“Shugaba Bola Tinubu ya sake jaddada kudirinsa na kyautata rayuwar ma’aikatan kasar nan ta hanyar sanya hannu kan kudurin karin albashi da alawus ga ma'aikatan shari'a.
“Wannan mataki ya nuna kwazon Tinubu na tabbatar da cewa kowane ma'aikaci a Najeriya, musamman masu aiki a muhimman wurare sun samu albashin da ya cancanta."
"Ta hanyar ba da fifiko ga walwalar ma'aikatan shari'armu, shugaban kasa ya kara karfafa amincin tsarin shari'a da kafa sabon tsarin shugabanci wanda ke mmutunta ma'aikata."
Albashin alkalai: Tinubu ya aikawa majalisa sako
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya bukaci majalisar dattawa ta kawo kudirin da zai sake fasali kan albashi da alawus na ma'aikatan shari'a.
A cikin wasikar da Tinubu ya aikawa majalisar, wanda Godswill Akpabio ya karanta, shugaban kasar ya ce karawa ma'aikatan shari'a albashi zai kawo gyara da inganta bangaren shari'ar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng