Ayyuka 5 da Gwamna Abba Ya Kashewa N700m domin Magance Matsalar Ruwan Kano
- Gwamna Abba Yusuf ya dauki wasu matakan ganin ya magance matsalolin ruwa da ake fama da shi a birni da kauyukan Kano
- Gwamnantin Kano ta kashe kimanin Naira miliyan 700 domin aiwatar da wasu ayyuka biyar na samar da ruwa a sassan jihar
- A yayin da wasu ayyukan tuni aka kammala su, wasu kuma har yanzu ana kan gudanar da su kamar jan bututun ruwa zuwa Kumbotso
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnatin Kano ta dauki wasu muhimman matakai na ganin ta magance matsalar ruwa da ake fama da ita na tsawon shekaru a sassan jihar.
Gwamna Abba Yusuf, tun bayan hawansa mulki ya sha alwashin yin duk mai yiyuwa domin ganin ruwan sha ya wadata a birni da kauyukan Kano.
A wani rahoto da shafin @AKYMediaCenter a dandalin X ya fitar, an zayyana wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar ta aiwatar kan ruwan sha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya nuna cewa Gwamna Abba Yusuf ya kashe kimanin Naira miliyan 700 domin aiwatar da wadannan ayyuka, wadanda wasu an kammala wasu kuma an kusa.
Ayyuka 5 na magance matsalar ruwan Kano
1. Samar da famfunan ruwa
Daya daga cikin matakan da gwamantin Kano ta dauka shi ne samar da sababbin famfunan ruwa guda 10 ga cibiyoyin tace ruwa na Tamburawa/Challawa
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Gwamnan Abba ya amince da samar da famfunan da za su ci N502,000,000 a yayin wani zaman majalisar zartarwar jihar Kano.
2. Samar da rijiyoyin burtsatse
Aiki na biyu shi ne na samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana a cikin garuruwan da ke da matsananciyar buƙata a duk faɗin Albasu, Tsanyawa da Dambatta.
SolaceBase ta ruwaito mazauna yankin sun ce sama da shekaru 40 suke rayuwa ba tare da samun tsaftataccen ruwan sha ba.
3. Gyara rijiyar burtsatse a Sheka
An kuma ruwaito cewa gwamnatin Abba Yusuf ta gyara rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana a Sheka, Gidan Malam.
Rahoton shafin @AKYMediaCenter ya nuna cewa gwamnati ta kammala wannan aiki.
4. Jan bututun ruwa a Kumbotso
An ce Gwamna Yusuf ya fitar da kudi domin jan bututun ruwa zuwa Unguwar Yanshana da Unguwar Rimi da ke karamar hukumar Kumbotso.
Rahoton ya ce har yanzu ana kan yin wannan aiki, amma da sa ran zuwa nan kwanaki biyar za a kammala.
Wadannan ayyukan da suka kai kimanin Naira Miliyan 700 an yi su ne domin tabbatar da samar da wadataccen ruwan sha ga gidaje, ofisoshi da sauran harkokin kasuwanci a fadin jihar Kano.
"Muna kashe N1.2bn kan ruwa" - Kwamishina
A wani labarin, mun ruwaito cewa kwamishinan albarkatun ruwa na Kano, Ali Makoda, ya ce gwamnatin jihar na kashe Naira biliyan 1.2 a kowanne wata kan ruwan sha.
Ali Makoda ya ce gwamnatin jihar na kashe kudin wajen sayen dizal na N400m, sinadaran gyara ruwa na N387m da kuma biyan kudin wutar lantarki da N280m da sauran dawainiyoyi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng