Buhari ya Koma Fadar Aso Rock a Karon Farko, Shi da Jonathan Za su Gana da Tinubu

Buhari ya Koma Fadar Aso Rock a Karon Farko, Shi da Jonathan Za su Gana da Tinubu

  • A yau Talata ne Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya shirya taron majalisar magabata na kasa a fadar shugaban kasa
  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa fadar a karon farko tun saukarsa a mulkin Nijeriya a shekarar 2023
  • Taron zai hada da tsofaffin shugabannin Najeriya domin ba shugaban kasa shawara wajen ganin Najeriya ta samu cigaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yanzu haka tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan sun isa fadar shugaban kasa.

Tsofaffin shugabannin za su tattauna ne a zaman majalisar magabata na kasa domin ba shugaban kasa shawara.

Buhari da Jonathan
Buhari da Jonathan sun isa fadar shugaban kasa domin ganawa da Tinubu. Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Cif Olusegun Obasanjo na cikin shugabannin da ba su halarci zaman na yau ba.

Kara karanta wannan

Equatorial Guinea: Tinubu zai shilla kasar waje kwanaki 4 bayan gama zanga zanga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin zaman majalisar magabata na kasa

A kan shirya zaman majalisar magabata na kasa ne domin ba shugaban kasa shawara kan wasu abubuwa da zai bijiro da su.

Wannan shi ne karon farko da shugaba Bola Tinubu ya shirya taron tun hawansa mulki a karon farko a shekarar 2023.

Buhari ya isa fadar shugaban kasa

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa fadar shugaban kasa domin zaman majalisar magabata.

Haka zalika Goodluck Ebele Jonathan na cikin manyan kasa da suka halarci taron da yanzu haka yake gudana.

Shugabannin da ba su samu zuwa ba

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo na cikin waɗanda ba su samu halartar zaman ba kwata kwata.

Sai dai jaridar Punch ta wallafa cewa Abdulsalami Abubakar da Yakubu Gowon za su halarci taron ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

Ana sa ran Buhari ya koma Aso Rock, Tinubu ya kira taron majalisar magabata na kasa

An gargadi Tinubu kan canja tsarin mulki

A wani rahoton, kun ji cewa masana sun tura sakon gargadi ga shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan canza tsarin mulkin Najeriya.

Alhaji Tanko Yakasai da Farfesa Auwalu Yadudu sun bukaci shugaba Bola Tinubu ya yi taka-tsan-tsan kan maganar canza tsarin mulkin.

Yadudu ya bayyana cewa a yanzu haka Najeriya ba ta cikin bukatar sabon tsarin mulkin kasa sai dai ana bukatar samun wanda za su yi adalci ne kawai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng