Zanga Zanga: Abba Ya Ziyarci Wurin da aka Lalata, Ya Daukarwa Kanawa Alkawari

Zanga Zanga: Abba Ya Ziyarci Wurin da aka Lalata, Ya Daukarwa Kanawa Alkawari

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar gani da ido wurin da aka lalata yayin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa
  • Abba Kabir Yusuf ya nuna takaici kan yadda aka lalata dukiya mai dimbin yawa da abubuwa masu muhimmanci a lokacin zanga zangar
  • Haka zalika Abba Gida Gida ya yi alkawari kan cewa gwamnatin jihar Kano za ta dauki matakin kawo gyara a wuraren da ka lalata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar gani da ido ma'ikatar shari'a da aka lalata a yayin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

A yayin ziyarar, gwamnan ya jaddada cewa yan daba da aka ɗauko haya ne suka yi barna a jihar yayin zanga zangar.

Kara karanta wannan

Dattawan Kudu sun raba gari da Tinubu kan kalamansa, siyasarsa ta samu koma baya

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano ya ziyarci ma'aikatar shari'a da aka lalata a yayin zanga zanga. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da Abba Kabir Yusuf ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya ziyarci ma'aikatar shari'a

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci ma'aikatar shari'a ta Kano domin ganin barnar da aka yi a wajen a lokacin zanga zanga.

Abba Kabir Yusuf ya zagaya wuraren da aka yi kone-kone da fashe-fashe tare da rakiyar jagororin ma'aikatar.

Abba ya nuna takaici kan kone kone

Abba Kabir Yusuf ya ce abin takaici ne matuka yadda aka lalata dukiya da wasu abubuwa masu muhimmanci a wajen.

Ya kuma tabbatar da cewa lamarin ya shafi ayyukan kotu a wajen ta inda ya jawo tsaiko kan gudanar da shari'a.

Abba ya yi alkawarin gyara ma'aikatar shari'a

Bayan ganin barnar da aka yi, Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin cewa za a gyara wajen fiye da yadda yake a baya.

Kara karanta wannan

Hauhawar farashi: Abba Gida Gida ya ji koken jama'a, gwamna ya sa labule da 'yan kasuwa

Dadin dadawa gwamnan ya ce ba za su bar wajen ya dade a lalace ba wanda hakan ke nuna cewa za a yi gyaran ma'aikatar cikin gaggawa.

An gano badakalar N50bn badakalar a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano ta yi bayani kan badakalar kudi da ta binciko na sama da Naira biliyan 50.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng