Musulmai da Kiristoci Sun Hada Kai Wurin Addu’o’i a Plateau, Sun Roki Gwamnati

Musulmai da Kiristoci Sun Hada Kai Wurin Addu’o’i a Plateau, Sun Roki Gwamnati

  • Yayin da ake cikin halin damuwa na rashin ruwan sama a wasu wurare, Musulmai da Kiristoci sun koma ga Allah
  • Addinan guda biyu sun bayyana damuwa kan yadda zunuban al'umma suka yi yawa wanda ke haka samun ruwan sama
  • Hakan na zuwa ne yayin da jihohi da dama ke fama da rashin ruwan sama wanda ka iya jawo matsala ga amfanin gona

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Daruruwan Musulmai da Kiristoci ne suka fito neman mafita kan rashin ruwan sama a jihar Plateau.

Mabiya addinan guda biyu sun taru ne a wurare daban-daban domin rokon ubangiji kan matsalar rashin ruwa a jihar.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya yi nasara, kotu ta yanke hukunci kan masu zanga zanga

Musulmai da Kiristoci sun koma ga Allah saboda rashin ruwan sama
Rashin ruwan sama ya tilasta Musulmai da Kiristoci hada kai wurin gudanar da addu'o'i. Hoto: Legit.
Asali: Original

Ruwa ya maida Musulmai, Kiristoci ga Allah

Musulmai sun taru ne a filin Idi yayin da Kiristoci kuma suka taru a coci-coci domin kaskantar da kai ga Ubangiji, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa amfanin gona da dama sun fara lalacewa saboda rashin ruwa da ake tunanin zai gurgunta tattalin arziki.

Shugabannin addinai da suka halarci addu'o'in sun bukaci al'umma su gyara tsakaninsu da Ubangiji da cewa shi ne silar rashin ruwa.

Plateau: Jan kunne daga malaman Musulunci & Kiristoci

Babban limamin masallacin Juma'a a Yelwa, Abdulkareem Salihu ya bayyana muhimmancin tsoron Allah.

Sheikh Salihu ya ce hakan ne matakin farko da mutum zai roki Allah kuma ya amsa masa bukatunsa inda ya ce zunuban da ake aikatawa kamar takalar Allah SWT ne da zai iya jawo fitina a kasa.

Kara karanta wannan

An shiga jimami a Arewacin Najeriya, mata da miji da 'ya'yansu 5 sun mutu bayan cin rogo

Faston cocin RCC a Lakichi, Isaac Luka ya ce kashe-kashe da cin amana da zubar da ciki na daga cikin zunuban da ke jawo matsala.

Malaman addinan sun bukaci gwamnati da ta yi mai yiwuwa wurin inganta rayuwar al'umma domin sauke nauyin da aka daura musu.

CAN-Taraba ta bukaci addu'o'i da azumi

Kun ji cewa kungiyar matasa ta CAN a jihar Taraba ta bukaci al'ummar Kiristoci da su fita addu'o'i da kuma yin azumi.

Hakan na zuwa ne yayin da aka kwashe kwanaki ba tare da samun ruwan sama ba da hakan ke kawo cikas ga amfanin gona.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.