Basarake Ya Sha Yabo da Ya Kayyade Farashin Kaya, Ya Gargadi 'Yan Kasuwa
Yayin da jama'a ke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa, wani basarake ya dauki mataki kan 'yan kasuwansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- Ewi na Ado-Ekiti, Oba Rufus Adejugbe ya haramta kungiyoyin 'yan kasuwa da ke tsauwalawa mutane kan tsadar kaya
- Legit Hausa ta yi magana da wani dan kasuwa a jihar Gombe kan wannan mataki game da tsadar kaya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ekiti - Fitaccen basarake a jihar Ekiti ya dauki muhimmin mataki kan tsadar kayayyaki da ake fama da shi a kasar.
Sarkin Ado-Ekiti, Oba Rufus Adejugbe ya haramta kasancewar kungiyoyin 'yan kasuwa a birnin Ado-Ekiti da ke jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsadar kaya: Basarake ya kayyade farashi
Basaraken a Ekiti ya ba da umarnin ne yayin ganawa da shugabannin kasuwa a jiya Litinin 12 ga watan Agustan 2024, cewar Punch.
Oba Adejugbe ya kuma umarci duka 'yan kasuwar ka da wani ya kuskura ya siyar da kaya fiye da farashin da aka gindaya.
Sarkin ya gargadi wadanda abin ya shafa da su tabbatar sun bi umarnin inda ya ce ba za a sassautawa wadanda suka ketare dokar ba.
Yadda Sarki ya yanke farashin kaya
Daga cikin umarnin shi ne siyar da kilon nama da bai zai wuce N4,500 ba sai garri N700 da ganye N50 kacal da kuma tattasai N100, Premium Times ta tattaro.
"Mun samu labarin yadda 'yan kasuwa ke kara kudin kaya musamman ganye da tattasai da gari da nama da wake da sauransu wurin tsauwalawa jama'a.
"Mun dauki matakai domin sassautawa al'umma kuma sarakuna za su na bi domin tabbatar da an bi umarnin yadda ya kamata."
"Duk wanda muka samu da saba umarni ko dokar da aka gindaya zai fuskanci hukunci mai tsanani."
- Oba Rufus Adejugbe
Legit Hausa ta yi magana da wani dan kasuwa a jihar Gombe kan wannan mataki game da tsadar kaya.
Alhaji Abubakar Mohammed ya ce yana da kyau a samu saukin kaya amma kayyade farashi ga yan kasuwa ba shi ne mafita ba.
"Dan kasuwa ne ya san nawa ya sayi kaya domin haka shi zai fadi farashin da zai ci riba."
"Kowa yana son a samu sauki a rayuwa amma fa idan man fetur na tsada dole komai ya tashi saboda dauko kaya da sauran dawainiya."
- Abubakar Mohammed
Basarake ya tsira daga hannun 'yan bindiga
Kun ji cewa Alara na Ara-Ekiti a ƙaramar hukumar Ikole ta jihar Ekiti, Oba Adebayo Fatoba ya bayyana yadda ya yi nasarar tserewa daga ƴan bindiga.
Hakan ya biyo bayan kisan sarakuna a Ekiti guda biyu, Onimojo na Imojo, Oba Olatunde Olusola da Elesun na Esun Ekiti, Oba Babatunde Ogunsakin.
Asali: Legit.ng