Muhimman Abubuwa 3 da suka Faru a Arewa bayan Zanga Zangar Tsadar Rayuwa

Muhimman Abubuwa 3 da suka Faru a Arewa bayan Zanga Zangar Tsadar Rayuwa

  • Abubuwa da dama sun faru a Arewacin Najeriya tun bayan zanga zangar tsadar rayuwa da aka fara a ranar 1 ga watan Agusta
  • Daga cikin abubuwan da suka faru a Arewacin Najeriya wasu sun shafi talakawa, wasu masu mulki wasu kuma yan kasuwa
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku muhimman abubuwa guda uku da suka faru kuma suka ja hankula bayan zanga zangar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ta haifar da abubuwa da dama a Arewacin Najeriya.

Komawa zuwa ga adduo'i na daya daga cikin abubuwan da suka ja hankalin al'umma a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kano: Bidiyon yadda aka yi salloli da addu'o'in neman mafita kan tsadar rayuwa

Arewa
Maynan abubuwa da suka ja hankali a Arewa bayan zanga zanga. Hoto: Mubark Lawal Ibrahim
Asali: Facebook

A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku muhimman abubuwa guda uku da suka ja hankalin al'umma a Arewacin Najeriya bayan zanga zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Komawa ga adduo'i

Bayan kammala zanga zanga, al'ummar Arewa sun koma karatun Al-Kur'ani, sallah da adduo'i musamman a jihar Kano.

An gudanar da adduo'i, saukar Al-Kur'ani da salloli a jihohin Arewa domin kawo ƙarshen zalunci da azzalumai a fadin Najeriya

2. Tsadar kayayyaki a kasuwanni

Bayan kammala zanga zanga, an fuskanci tashin farashin kayan masarufi wanda ya kai ga zama tsakanin yan kasuwa da gwamnatin Kano.

Wannan na cikin abubuwan da suka ja hankalin al'umma wanda wasu ke ganin zanga zangar ba ta yi amfani ba tunda dama an yita ne domin neman sauki.

3. Maganar mataimakin shugaban kasa

Biyo bayan kammala zanga zangar, Sanata Kashim Shettima ya yi kira na musamman domin neman hadin kan yan Arewa.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe budurwa mai shirin zama amarya da wasu matasa a zanga zanga a Arewa

Mataimakin shugaban kasa ya yi kiran ne yana mai cewa zanga zangar ta bayyana babban kalubalen da yake gaban shugabannin Arewa kuma ya kamata su magance su.

Zanga zanga: Shettima ya yi kira ga matasa

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya sha alwashin cigaba da tafiya da matasa a wannan gwamnati.

Kashim Shettima ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da cigaban matasan Najeriya domin su dogara da kansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng