An Shiga Tashin Hankali a Arewa: 'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Makaranta da wasu 7
- Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane bakwai aka kashe a kauyen Sai da ke kan hanyar Takum zuwa Wukarin a jihar Taraba
- An ruwaito wasu 'yan bindiga ne dauke da makamai suka tare wata motar fasinja inda suka mutum bakwai ciki har da shugaban makaranta
- Wani manomi da abin ya faru kan idonsa ya ce bayan 'yan ta'addan sun kashe matafiyan, sun kuma farmaki manoman da ke aiki a gonakinsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Taraba - Akalla fasinjoji bakwai da suka hada da shugaban makaranta da direba sun mutu a kauyen Sai da ke kan hanyar Takum zuwa Wukari a jihar Taraba.
An kuma ruwaito cewa wasu fusatattun matasa sun kashe wasu uku a garin Takum, hedikwatar karamar hukumar Takum ta jihar Taraba, sakamakon kisan matafiyan.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa shugaban makarantar, Mista Samuel Mbapuun, an dauke shi daga GDSS Takum zuwa karamar hukumar Ibi na jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taraba: 'Yan bindiga sun kashe matafiya
An ce shugaban makarantar tare da sauran mutanen suna tafiya ne lokacin da ‘yan bindigar suka fito daga daji dauke da bindigu tare da budewa motar wuta.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa bayan kashe fasinjojin bakkwai, 'yan bindigar sun kuma kai farmaki kan manoman da ke aiki kusa da inda fasinjojin bakwai suka mutu.
Wata majiya ta ce bayan harin da aka kai a kauyen Sai, wasu fusatattun matasa daga garin Takum sun fara tayar da tarzoma lamarin da ya kai ga kashe mutane uku.
Manomi ya fadi yadda abin ya faru
Wani manomi wanda harin ya rutsa da shi, Mista Iorapuu Pila, wanda ya zanta da 'yan jarida ta wayar tarho, ya ce ‘yan bindigar sun fito ne daga dajin da ke kusa da kauyen Sai.
Mista Pila, wanda a halin yanzu yake karbar magani a wani asibiti a garin Sai, ya ce shi da wasu suna cikin aiki a gonakinsu 'yan ta'addan suka budewa motar fasinjojin wuta, tare da farmakarsu.
"Kafin mu gudu daga wurin, wasu daga cikin 'yan fashin sun tunkaro inda muke, suka far mana da adduna, mutum tara daga cikin mu sun jikkata."
- A cewar manomin.
'Yan bindiga sun kashe sojan Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe Kyaftin Ibrahim Yohana, wani jajurtaccen sojan Najeriya dan asalin jihar Kaduna wata tara bayan aurensa.
An ce abokan aikin Kyaftin Ibarahim sun bayyana shi a matsayin babban jami’i mai hazaka wajen gudanar da aikinsa wanda yake shiga a gaba wajen kare rayukan jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng