WAEC Ta Fitar da Sakamakon Jarabawar WASSCE ta 2024, Ta Fadi Yadda ake Dubawa

WAEC Ta Fitar da Sakamakon Jarabawar WASSCE ta 2024, Ta Fadi Yadda ake Dubawa

  • Hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta fitar da sakamakon jarrabawar kammala sakandare (WASSCE) ta 2024
  • Kimanin dalibai 1,814,344 ne daga makarantun sakandare 22,229 a fadin kasar nan ne aka ce sun zana jarrabawar WASSCE 2024
  • Kamar yadda sanarwar da WAEC ta fitar a ranar Litinin, daliban da suka zana jarabawar za su iya duba samakonsu a shafin hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Yaba, jihar Legas - Hukumar WAEC ta sanar da fitar da sakamakon jarrabawar kammala sakandare ta Afirka ta Yamma (WASSCE) na shekarar 2024.

A ranar Litinin, 12 ga watan Agusta, 2024 ne hukumar WAEC ta ba da dama ga dalibai su duba sakamakon jarabawar.

Kara karanta wannan

WASSCE 2024: WAEC ta rike sakamakon jarabawar dalibai 215,267, ta fadi dalili

Yadda dalibai za su duba sakamakon jarabawar WASSCE 2024
WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar WASSCE ta shekarar 2024. Hoto: Waec Nigeria, Covenant University
Asali: Facebook

WAEC ta saki sakamakon jarrabawar WASSCE 2024

An fitar da sanarwar ne a shafin WAEC na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar hukumar ta bayyana cewa:

"Hukumar jarrabawar Afirka ta Yamma tana farin cikin sanar da daliban da suka zana WASSCE ta 2024 cewa an fitar da sakamakon jarabawar a yau Litinin, 12 ga Agusta, 2024."

Legit Hausa ta fahimci cewa, kimanin dalibai 1,814,344 ne daga makarantun sakandare 22,229 a fadin kasar nan suka zana jarrabawar WASSCE 2024.

Yadda ake duba jarabawar WASSCE 2024

Ta hanyar amfani da wayarku ko kwamfuta, za ku ziyarci shafin https://waecdirect.org domin duba sakamakon jarabawarku.

  • Shiga bangaren duba sakamakon jarabawar a shafin yanar gizon WAEC www.waecdirect.org.
  • Shigar da lambar jarrabawarku
  • Zaɓi watan jarabawar, misali Mayu/Yuni
  • Zaɓi shekarar jarabawa, misali 2024
  • Ba da amincewarka domin ganin sakamakon.

Domin duba sakamakon WAEC ɗin ku, a lura cewa ƙila kuna buƙatar katin WAEC don dubawa. Sai ku bi matakan da muka zayyana a sama.

Kara karanta wannan

Ana rade radin gwamnan PDP zai sauya jam'iyya, tsageru sun jefa 'bam' ofishin APP

Shugaban makaranta ya ci kudin WAEC

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani shugaban makaranta ya tattara kudin da aka tattara masa na jarawabar WAEC din daliban makarantar ya tsere da su a jihar Oyo.

Wasu iyaye da su ka ci karbo rancen kudi domin biyawa yaransu kudin zana jarrabawar sun nuna tashin hankalin da suka bayan samun labarin guduwar shugaban makarantar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.