Kwamishinan Ganduje Ya Gaskata Dan Bello, Ya Tabbatar da Badakalar Murtala Garo
- Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Mu'azu Magaji ya gasgata rahoton da Dan Bello ya fitar cewa Murtala Garo ya saci kudin jama'a
- Dan Bello ya yi ikirarin cewa tsohon kwamishinan kananan hukumomi lokacin Ganduje ya saci N10bn ya sayi kadara a birnin Makkah
- Mu'azu Magaji ya ce ko a lokacin da ya ke kwamishina sai da ya kori kamfanin Murtala Garo, lamarin da ya jawo rigimarsa da matar Ganduje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Mu'azu Magaji, tsohon kwamishinan ayyukan na Kano a lokacin gwamnatin tsohon gwamna Abdullahhi Umar Ganduje ya magantu kan bidiyon Dan Bello.
A cikin wani bidiyo da Dan Bello (wanda asalin sunansa Bello Habib Galadanchi) ya fitar, ya zargi tsohon kwamishinan Kano, Murtala Sule Garo da satar kudin gwamnati.
Dan Bello ya zargi Murtala da rashawa
A cikin bidiyon wanda Dan Bello ya wallafa a shafinsa na X, ya yi ikirarin cewa Murtala Sule Garo ya saci akalla Naira biliyan 10 a lokacin da yake kwamishinan kananan hukumomi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bello ya yi ikirarin cewa Murtala Garo ya rika karbar Naira miliyan 5 daga kowace karamar hukumar Kano a duk wata da sunan za a biya kudin dizal na ruwan da ake tacewa a jihar.
Sai dai Dan Bello ya ce babu dizal din da ake saya domin Murtala Garo na amfani da kamfanoninsa biyu, MJ da AU a matsayin wadanda ke sayarwa gwamnati man.
Bello ya ce MJ da AU na turawa wasu 'yan canji a kasuwar Wapa kudin domin mayarwa zuwa Riyal, inda ake turawa kamfanin 'Next Vision' da ke birnin Makkah.
A cewar dan jaridar, kamfanin N.V ya sayawa Murtala Garo wani bangare na wani babban otel a kusa da dakin Ka'abah, bayan da tsohon kwamishinan ya tura akalla Naira biliyan 10.
Kwamishinan Ganduje ya gaskata Dan Bello
Bayan fitar wannan bidiyo na Dan Bello, 'yan soshiyal midiya sun cika da mamakin irin badakalar da tsohon kwamishinan Kano ya tafka, inda wasu ke ganin karya ce kawai.
Sai dai tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, Mu'azu Magaji, ya gaskata rahoton Dan Bello, inda ya ce badakalar ce ta hada shi fada da uwar gidan Ganduje.
A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, tsohon kwamishinan ayyukan ya ce:
"Kai jama’a, shin da sauran imani kuwa? Koda yake daga na gaba ake gane zurfin ruwa.
"Mu je zuwa! Mun yi ta babatu kan wannan dan halin a gwamnatin mu amma aka mai damu mahaukata. Asali ma saida aka ga bayanmu kan ba a son jin gaskiya. To an zo wurin!"
Wani Sulaiman Musa Tofa ya tambayi Mu'azu: "Jagora na ga kaima ka rike kwammishinan ayyuka a baya," sai jagoran na 'Win Win' ya ba shi amsa da:
"Ai ko ni shaida ne don sai da na kori wannan kamfanin a ma'aikatar ayyuka kan badakalar dizal, wannan dama wasu dalilan sune farkon rigimar mu da Gwaggo."
Kalli bidiyon Dan Bello a nan kasa:
'Dan El-Rufai ya ba Dan Bello shawara
A wani labarin, mun ruwaito cewa daya daga cikin 'ya'yan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya nemi Dan Bello (Bello Galadanchi) da ya yi hattara da 'yan siyasa.
Bashir El-Rufai ya ce ya kamata Dan Bello ya rika bi a hankali a bidiyoyin fallasa 'yan siyasa da yake yi, la'akari da cewa shi kansa yana cikin masu son tsohon dan jaridar.
Asali: Legit.ng