Abuja da wasu Jihohi 27 da har Yanzu ba Su Kafa Kwamitin Aiwatar da Sabon Albashi ba

Abuja da wasu Jihohi 27 da har Yanzu ba Su Kafa Kwamitin Aiwatar da Sabon Albashi ba

  • A halin yanzu, wasu jihohi sun jinkirta aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma'aikatansu
  • Legas na biyan ma'aikata N77,000 yayin da Edo ke biyan N70,000 tun kafin Tinubu ya rattaba hannu kan dokar sabon albashi
  • Sai dai kuma jihohin Filato, Kebbi, Bayelsa, Delta da wasu jihohi 21 ba su kafa kwamitocin aiwatar da sabon albashi na N70,000 ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihohi 27 da babban birnin tarayya Abuja har yanzu ba su kafa kwamitocin aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 da aka amince da shi ba.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan sabon mafi karancin albashi a ranar 29 ga Yuli, 2024, bayan cimma matsaya da shugabannin kungiyoyin kwadago.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jigon PDP ya fadi yadda Tinubu zai magance matsalolin Najeriya

Jerin jihohi 27 da har yanzu ba su kafa kwamitin sabon albashi ba.
Albashin ma'aikatan Legas ya haura N70,000 yayin da ake biyan ma’aikatan Edo N70,000. Hoto: Governor Godwin Obaseki, Babajide Sanwo-Olu
Asali: Facebook

Wani abin mamaki shi ne, wasu jihohin kasar ba su fara shirin aiwatar da tsarin albashin da aka amince da shi ba, jaridar The Punch ta ruwaito a ranar Lahadi, 11 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wasu jihohi bakwai sun kafa kwamitocin aiwatarwa amma jihohin Legas da Edo ne kawai suka fara biyan sabon albashin.

Jihohin da ba su fara biyan N70,000 ba

Jihohin su ke:

  1. Plateau
  2. Kebbi
  3. Sokoto
  4. Nasarawa
  5. Bayelsa
  6. Delta
  7. Osun
  8. Ekiti
  9. Zamfara
  10. Benue
  11. Enugu
  12. Taraba
  13. Gombe
  14. Kogi
  15. Enugu
  16. Adamawa
  17. Niger
  18. Anambra
  19. Imo
  20. Ebonyi
  21. Oyo
  22. Akwa Ibom
  23. Bauchi
  24. Katsina
  25. Kaduna
  26. Cross River
  27. Yobe

Jihohin da suka kafa kwamitin sabon albashi

Sai dai wasu jihohi bakwai sun kafa kwamitocin aiwatarwar. Duk da haka, Legas da Edo ne kawai suka ce sun fara biyan mafi karancin albashin.

Jihohin su ne:

Kara karanta wannan

Kudin da kowane gwamna ya tashi da su da Tinubu ya raba Naira biliyan 430 a jihohi 34

  1. Kano
  2. Kwara
  3. Ogun
  4. Borno
  5. Jigawa
  6. Ondo
  7. Abia

Albashi: Jihohin da suka fara biyan 70,000

Legas da Edo

Kwamishinan yada labaran Legas, Gbenga Omotoso, a ranar Asabar, ya shaidawa manema labarai cewa jihar ta na biyan fiye da mafi karancin albashi tun kafin ta zama doka.

Gwamnatin jihar Edo karkashin jagorancin gwamna Godwin Obaseki ta ce ta fara biyan mafi karancin albashi, inji rahoton Arise News.

Kwara: Gwamna ya kafa kwamitin karin albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna AbdulRahman AbdulRasaq ya dauki matakin aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000 a jihar Kwara.

Gwamna AbdulRazak ya kafa kwamiti mai mutane 21 domin yin nazari tare da ba da shawarar yadda ya kamata jihar ta rika biyan sabon mafi karancin albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.