An Barke da Murna da Fitaccen Dan Kasuwa a Arewa Ya Rage Farashin Siminti
- Wani mai amfani da kafar sadarwa ta X ya wallafa cewa kamfanin siminti na Dahiru Mangal ya fara siyar da siminti a farashi mai sauki
- Matashin mai suna Maleek Anas ya wallafa a shafin X cewa ya sayi buhunan siminti guda biyu kan kudi N6,000
- Wasu mutane da dama sun fara bincikar wurin da za su samu damar siyan simintin yayin da ake fama da tsadar rayuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Fitaccen dan kasuwa a Najeriya, Dahiru Mangal ya fara siyar da siminti a kamfaninsa da ke jihar Kogi.
Kamfanin mai suna Mangal Cement Company mallakar attajiri dan jihar Katsina an kashe masa kudi kimanin $1.5bn.
Matashi ya fadi yadda ya sayi siminti
Wani mai amfani da kafar sadarwa ta X, Maleek Anas ya wallafa wasu buhunan siminti guda biyu da ya siya a farahin mai rahuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Anas ya wallafa buhunan guda biyu inda ya ce ya sayi kowane kan N6,000 kacal a kamfanin.
"Farashin simintin Mangal N6,000 kacal ake siyarwa."
- Maleek Anas
Siminti: Mutane da dama sun yi martani
@Melebroz 1:
"Wannan mataki ne mai kyau, sai dai ina tunanin kamfanin Mangal ba zai iya samar da siminti buhuna 200 ba a rana."
@YDutsun44451:
Muna godiya Mangal da ka kawo gasa a kasuwancin siminti, ya kamata ka rage farashin saboda ka kara samun kwastomomi."
@de_profde_chef:
Shin za a iya ragewa zuwa N4,000 kacal? sannan ya yanayin karfin simintin yake."
@Abbadanejo:
"Ina son siyan buhu 50, shin akwai wanda zai taimakamin da haka?"
Kamfanoni sun ki rage farashin siminti
A wani labarin, Kwamitin da ke bincike kan farashin siminti ya bayyana halin da ake ciki kan zama da majalisar wakilai za ta yi da kamfanonin siminti.
A ranar Litinin 20 ga watan Mayun 2024 Majalisar ta gayyaci manyan kamfanonin domin su gurfana a gabanta kan shawo tsadar siminti a Najeriya.
Shugaban kwamitin binciken farashin siminti da majalisar ta kafa, Jonathan Gaza Gefwi ya ce suna fakewa da umurnin kotu wurin kin amsa gayyatarsu.
Asali: Legit.ng