Zanga Zanga: Matasa Sun Aiki Gwamna da Sako zuwa ga Tinubu, Sun Zayyana Bukatunsu

Zanga Zanga: Matasa Sun Aiki Gwamna da Sako zuwa ga Tinubu, Sun Zayyana Bukatunsu

  • A rana ta 10 ta kammala zanga-zangar yunwa da aka fara daga 1 ga watan Agusta, matasan jihar Filato sun rubuta takarda dauke da bukatunsu
  • An ce matasan sun gana da gwamnan jihar, Caleb Mutfwang inda suka mika masa takardar bukatun tare da cewar zai kai wa Tinubu
  • Bukatun matasan sun hada da neman gwamnatin Filato ta rage kashe kudin gwamnati yayin da aka nemi Tinubu ya mayar da fetur N300

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - A ranar Asabar, 10 ga watan Agusta da aka kawo karshen zanga-zangar yunwa a fadin kasar nan, matasan Filato sun gana da gwamnansu, Caleb Mutfwang.

Gamayyar kungiyoyin matasan jihar sun gabatar da takardar bukatunsu ga Gwamna Mutfwang a Jos domin mikawa shugaban kasa Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Yunwa na barazana ga rayukan almajiran Kano, an roki matasa su hakura da zanga zanga

Matasan Filato sun aiki Gwamna Mutfwang ya kaiwa Tinubu sakon bukatunsu
Filato: Matasa sun mika bukatunsu ga gwamna da cewar zai kaiwa Tinubu. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Zanga-zanga ta rikide zuwa tashin hankali

Jaridar The Punch ta bayar da rahoton cewa, mazauna jihar Filato sun gudanar da zanga zanga a manyan titunan Jos a wani bangare na zanga-zangar da ake yi a fadin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai daga baya wasu ‘yan baranda sun kwace zanga-zangar lumanar inda suka fara 'satar kayayyaki' da lalata dukiyoyin gwamnati da na jama’a.

Wannan lamari ya sa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a babban birnin Jos da Bukuru.

Matasa sun ba gwanna sako ga Tinubu

Da ya ke gabatar da takardar a madadin matasan, wakilinsu, Mista Sam Ode, ya bayyana cewa bukatun sun shafi gwamnatin jihar da kuma ta tarayya, inji rahoton Daily Trust.

“Muna bukatar gwamnatin Filato ta gaggauta rage kudin gudanar da mulki. Muna neman bayani kan yadda aka yi amfani da kaya da kudaden tallafi da ake samu daga tarayya.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Majalisar matasan Arewa ta yi fatali da neman dauke cibiyar NCC daga Kano

“Muna kara kira ga gwamnatin jihar da ta aiwatar da mafi karancin albashin N70,000 tare da rage kudin makarantun manyan makarantu.
"Ga gwamnatin tarayya kuwa, muna kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya kawo karshen cin hanci da rashawa, ya mayar da farashin man fetur zuwa N300 sannan ya rage kudin wutar lantarki."

Mista Ode ya ce yana so shugabannin su sani cewa wadannan bukatu burin jama'a ne na neman hanyar samun ci gaba mai dorewa ba wai adawa da gwamnati ba.

An sassauta dokar hana fita a Filato

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Filato ta sassauta dokar hana fita ta awa 24 da ta kakabawa a manyan biranen jihar sakamakon zanga-zangar yunwa.

Bisa umarnin Gwamna Caleb Mutfwang, an ba jama'a damar fitowa su gudanar da harkokinsu daga ƙarfe 12:00 na rana zuwa ƙarfe 6:00 na yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.