Ana Tsaka da Bankadar Dan Bello, Tinubu Ya Dakatar da Aikin Hanyar Kano Zuwa Maiduguri
- Gwamnatin Tarayya ta dakatar da wani bangare na aikin babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri saboda sakaci na 'yan kwangila
- Gwamnatin ta dakatar da aikin ne saboda yadda ya dauki lokaci mai tsayi ba tare da cimma wani abu ba daga 'yan kwangila
- Ministan Ayyuka, Dave Umahi shi ya tabbatar da haka inda ya ce lokacin nade hannu kan bata lokaci kan gina hanyoyi ya wuce
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta dakatar da aikin wani bangare na hanyar Kano zuwa Maiduguri saboda bata lokaci.
Gwamnatin ta dauki matakin ne saboda yadda 'yan kwangilar suka dauki lokaci mai tsawo ba tare da wani cigaba ba.
An dakatar da aikin Kano zuwa Maiduguri
Ministan Ayyuka a Najeriya, Dave Umahi shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Umahi ya fadi haka ne ta bakin hadiminsa, Uchenna Orji a yau Asabar 10 ga watan Agustan 2024 da muke ciki.
Kwangilar an ba da ita ne ga kamfanin Dantata & Sawoe Ltd a shekarar 2007 wanda aka yi ta samun matsala kan aikin, Leadership ta tattaro.
Ministan ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da aikin inda ya ce hakan zai shafi 'yan Najeriya masu amfani da hanyar.
"A matsayina na Minista ina ga ya kamata kowa ya dauki laifin da ya yi, ba za mu nade hannayenmu mu bar aiki na tafiyar hawainiya ba."
"Yan Najeriya suna shan wahala musamman wadanda ke bin wannan hanya, Bola Tinubu yana duk mai yiwuwa domin inganta hanyoyin kasar."
- Dave Umahi
Kotu ta ba da umarni kan kananan hukumomi
Kun ji cewa Kotun Koli da ke Abuja ta sake ba da umarni bayan hukuncin da ta yi kan 'yancin kananan hukumomi bayan korafin Gwamnatin Tarayya
Kotun ta umarci ba kansiloli da shugabannin kananan hukumomi a Najeriya wa'adin shekaru hudu kamar yadda gwamnonin jihohi ke yi
Wannan na zuwa ne bayan hukuncin da kotun ta yi kan ba kananan hukumomin 'yancinsu yayin da gwamnonin jihohi ke dakile su
Asali: Legit.ng