Kudin da Kowane Gwamna Ya Tashi da Su da Tinubu Ya Raba Naira Biliyan 430 a Jihohi 34
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta rabawa jihohi wasu makudan kudi a karkashin tsarin NG-Cares
- Gwamnonin Zamfara, Nasarawa, Filato da Gombe su na cikin wadanda suka samu kudi masu yawan gaske
- Ministan kasafin kudi ya fadawa duniya kason da aka aika, Anambra da Kaduna ne kadai ba samu kudin nan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja – Gwamnatin tarayya ta fitar da sama da N438bn, ta maidawa jihohi a karkashin wani tsarin farfado da tattalin arziki.
Jami’in yada labarai da hulda da jama’a na ofishin NG-Cares, Suleiman Odapu, ya tabbatar da haka a wani jawabi da ya fitar kwanaki.
Za a samu wannan bayani a adireshin NG-Cares na yanar gizo wanda daga cikin shi ne Legit ta hada rahoton abin da aka ba jihohi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zamfara ta fi kowa sa'ar kudin NG-Cares
Jihar Zamfara kamar yadda gwamna Dauda Lawal Dare ya sanar, ta fi kowa samun kaso mai tsoka daga wannan kudi, ta karbi N49bn.
Nasarawa da Filato duk daga Arewa maso tsakiya ne su ka zo na biyu da na uku. The Guardian ta tabbatar da wannan labari a rahotonta.
Jihohin da suka rasa kason NG-Cares
Jihohin Anambra da Kaduna ne kadai ba su samu komai daga kason ba domin ba su iya gabatar da wani sakamako da ake bukata ba.
Channels ta rahoto wasu gwamnoni sun karyata lamarin, su ka ce gwamnatin tarayya ba ta aiko masu da sisin kobo ba zuwa yanzu.
Kamar yadda Ministan kasafin kudi ya sanar a jaridar Daily Trust, ga abin da aka ba jihohi:
NG-Cares: Nawa aka rabawa jihohi?
1. Delta
N13,268,320,155.81
2. Abia
N12,175,577,893.70
3. Bayelsa
N10,830,587,695.70
4. Yobe
N10,172,244,387.67
5. Kwara
N9,915,101,215.91
6. Osun
N9,562,512,549.27
7. Bauchi
N7,304,665,994.92
8. Kogi
N6,903,713,160.77
9. FCT
N6,773,326,717.84
10. Ebonyi
N6,255,864,530.97
11. Enugu
N6,191,959,222.93
12. Kano
N6,154,448,839.35
13. Oyo
N5,966,675,258.19
14. Borno
N5,898,270,783.50
15. Jigawa
N5,770,132,061.00
16. Lagos
N5,569,060,730.14
17. Taraba
N5,508,762,972.80
18. Ekiti
N5,507,202,258.33
19. Edo
N5,122,103,650.09
20. Benue
N4,908,421,973.10
21. Akwa Ibom
N2,430,830,532.46
22. Ogun
2,125,069,028.52
23. Zamfara
N49,182,347,834.58
24. Nasarawa
N27,204,679,444.17
25. Plateau
N26,312,588,262.79
26. Gombe
N25,305,166,261.04
27. Kebbi
N21,589,480,398.09
28. Rivers
N19,517,766,804.45
29. Niger
N17,769,395,563.89
30. Bauchi
N17,535,952,985.60
31. Katsina
N15,455,420,486.35
32. Imo
N15,408,252,449.34
33. Sokoto
N14,177,508,862.60
34. Cross River
N20,670,241,709.19
35. Ondo
N13,925,262,355.18
Tarihin kirkiro jihohi a Najeriya
An samu rahoton yadda Janar Yakubu Gowon ya fara kirkiro jihohi a tarihi shekarar 1967 domin karya C. Odumegwu Ojukwu.
Kafin Ibrahim Babangida wanda aka fi sani da IBB ya bar mulki ya amince da karin jihohi sama da 10 a shekarar 1987 da 1991.
Asali: Legit.ng