Ba a Gama Zanga Zanga ba, Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin da Zai Girgiza Tinubu

Ba a Gama Zanga Zanga ba, Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin da Zai Girgiza Tinubu

  • An buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya kori shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, domin kaucewa gagarumar zanga-zanga
  • Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ne ya ba Shugaba Tinubu wannan shawarar a wani sabon saƙon da ya fitar a ranar Asabar, 10 ga watan Agusta
  • A cewar malamin, zanga-zangar da ake yi a ƙasar nan a halin yanzu, wasan yara ce kan abin zai taho nan gaba, sannan hanyar kaucewa hakan ita ce a kori Mele Kyari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara.

Primate Ayodele ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta korar shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, domin kaucewa gagarumar zanga-zangar da ke tafe.

Kara karanta wannan

Jerin jagororin zanga zanga da jami'an hukumar DSS suka cafke

Primate Ayodele ya ba Tinubu shawara
Primate Ayodele ya bukaci Tinubu ya kori Mele Kyari Hoto: @primate_ayodele, @OfficialABAT, @nnpclimited
Asali: Twitter

Babban faston ya ba da shawarar ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, 10 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malami ya yi hasashen sabuwar zanga-zanga

Primate Ayodele ya ce zanga-zangar da ake yi kan yunwa a faɗin ƙasar nan, wasan yara ce idan aka kwatanta da abin da ubangiji ya nuna masa zai faru nan gaba.

Malamin ya ci gaba da cewa, mafita ɗaya tilo wajen magance zanga-zangar da ke tafe ita ce a kori Mele Kyari daga muƙaminsa.

A kwanakin baya ne shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya zargi Mele Kyari da yin zagon ƙasa ga tattalin arzikin ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa kamfanin NNPCL yana ƙoƙarin ganin sabuwar matatar mai da ya gina ta ruguje saboda yawancin jami’an kamfanin na da matatun mai a ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Jerin ƙasashe 4 da zanga zanga ta kawo sauyin gwamnati a nahiyar Afirka

Wace shawara Ayodele ya ba Tinubu?

"Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata Tinubu ya yi idan yana son ya ga addu'ar ƴan Najeriya, shi ne ya kori shugaban kamfanin NNPCL, idan har zai yiwu a kore shi kafin ƙarshen wannan watan."
"Idan ba haka ba wata gagarumar zanga-zanga na nan tafe. Wannan zanga-zangar za ta iya sanyawa Tinubu ya rasa kujerarsa. Za ta iya sanyawa gwamnatin Tinubu ta kasa yin mulki."

- Primate Elijah Ayodele

Primate Ayodele ya caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele ya yi magana kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Malamin addinin ya bayyana cewa manufofin tattalin arziƙi na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sun yi tsauri kuma sun ƙara rura wutar wahalar da ake sha a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng