An Barke da Murna da Tsohuwar 'Yar Majalisar Tarayya ta Kubuta a Hannun Yan Bindiga
- Rundunar yan sanda a jihar Delta ta tabbatar da sako tsohuwar 'yar Majalisar Tarayya da aka sace a jihar a watan jiya
- Rundunar ta ce an sako Joan Onyemaechi ne da daren jiya Juma'a 9 ga watan Agustan 2024 bayan sace ta a karshen watan Yuli
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Bright Edafe ya fitar a yau Asabar 10 ga watan Agustan 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Delta - An barke da murna bayan tsohuwar 'yar Majalisar Tarayya ta kubuta daga hannun yan bindiga.
Yan bindiga sun yi nasarar sace Joan Onyemaechi ne a ranar 30 ga watan Yulin 2024 a jihar Delta.
Yan sanda sun tabbatar da kubutar Onyemaechi
Rundunar yan sanda a jihar ita ta bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Asabar 10 ga watan Agustan 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin rundunar, SP Bright Edafe ya ce an sako Onyemaechi ne a daren jiya Juma'a 9 ga watan Agustan 2024.
Yayin sace tsohuwar 'yar Majalisar, yan bindigan sun yi ajalin dan sanda mai gadinta da kuma direban motarta nan take.
"Tabbas an sako ta da daren jiya Juma'a."
- Bright Edafe
Delta: Yawan kudin fansa da aka buƙata
Leadership ta tattaro cewa dawowar Onyemaechi ke da wuya cikin birnin Asaba ta wuce wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.
Tun farko, masu garkuwa sun bukaci kudin fansa har N1bn, sai dai babu tabbacin ko an biya kudin ko sabanin haka.
Onyemaechi ta rike muƙamin kwamishina a ma'aikatar ilimin kere-kere a jihar na tsawon lokaci.
Tsohon dan Majalisar Tarayya ya rasu
Mun baku labarin cewa wani tsohon dan Majalisar Tarayya daga jihar Lagos, Wole Diya ya riga mu gidan gaskiya.
Diya ya rasu ne a jiya Juma'a 9 ga watan Agustan 2024 bayan fama da jinya na kankanin lokaci a jihar Lagos.
Wannan mutuwa na Diya na zuwa ne yayin da Majalisar ke cikin jimamin rashe-rashe da aka yi a yan kwanakin nan.
Asali: Legit.ng