Daga Bude Kasuwannin Kano Bayan Zanga Zanga, Farashi Ya Yi Tashin Gwauron Zabo

Daga Bude Kasuwannin Kano Bayan Zanga Zanga, Farashi Ya Yi Tashin Gwauron Zabo

  • Zanga-zanga a jihar Kano, kamar wasu jihohin Arewa ta jawo an sanya dokar hana zirga-zirga na wani lokaci saboda tsaro
  • Wannan ya sa farashin kaya ya fara hawa saboda jama'a sun saye kayan abincin da ke shagunan cikin unguwanninsu
  • Sai dai bayan bude kasuwannin, farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo fiye da yadda ya ke gabanin dokar kullen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Wasu 'yan kasuwa sun tsawwala farashin kayan masarufi bayan an bude kasuwanni sakamakon sassauta dokar zirga-zirga a jihar Kano.

An samu labarin yadda farashin kayan amfani yau da kullum ya fara saukowa gabanin tsunduma zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Kano: Mabarata sun shafe kwanaki da yunwa, sun nemi a janye zanga zanga

Kasuwa
Zanga-zanga ta jawo tashin farashi Hoto: Adam Abu-bashal/Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa ta gano jama'a da dama sun cika kasuwannin Kano domin sayen kayan abinci a kan farashi mai tsada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu bambancin farashi bayan zanga-zanga

'Yan kasuwa a Kano sun bayyana yadda aka samu tashin farashi bayan bude kasuwanni, Jaridar Blueprint ta wallafa labarin.

An samu hawan farashin ne saboda bukatar abinci da jama'a su kara yi saboda karancinsa a shaguna, kamar yadda yan kasuwar su ka fada.

Farashin fulawa da shinkafa ya hau

Wani dan kasuwar Singa, Sa'idu Abdullahi ya bayyana cewa buhun sukari mai nauyin kilo 50 da ake sayarwa a N80,000, yanzu ana sayarwa akan N82,000.

Ana sayar da buhun fulawa mai nauyin kilo 50 a kan N62,000 amma yanzu ya koma N70,000.

Ita kuma shinkafa mai nauyin kilo 50 da ake sayarwa 72, 000 yanzu ana sayar da ita akan N80,000.

Kara karanta wannan

Hauhawar farashi: Abba Gida Gida ya ji koken jama'a, gwamna ya sa labule da 'yan kasuwa

Tashin farashi: Gwamna ya gana da yan kasuwa

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta zauna da kungiyar 'yan kasuwar Kano saboda tsawwala farashin kayan amfanin yau da kullum.

Tun bayan sassauta dokar takaita zirga-zirga a jihar Kano ne yan kasuwa su ka fara cin karensu babu babbaka ta hanyar kara farashin kayan abinci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.