Shugaba Tinubu Ya Ba Jami'an Tsaro Umarni Yayin da Ake Ci Gaba da Zanga Zanga
- Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci kamfanonin da ke aikin haƙar ma'adanai su ba da fifiko wajen kula da lafiyar ƴan Najeriya
- Shugaban ƙasa Tinubu ya kuma umarci jami'an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba
- Tinubu ya bayyana cewa kawo ƙarshen masu haƙar ma'adanan ba bisa ƙa'ida ba zai taimakawa tattalin arziƙin ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen murƙushe masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin ƙasar nan.
Shugaba Tinubu ya ce akwai masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a faɗin ƙasar nan waɗanda tilas ne jami’an tsaro su ga bayansu.
Bola Tinubu ya ba da umarni
Shugaba Tinubu ya kuma ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa kamfanonin da ke haƙo ma'adanai sun ba da fifiko wajen kula da lafiyar ƴan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.
Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne lokacin da yayin da yake sauraron wata lacca da ɗaliban kwalejin tsaro ta ƙasa (NDC) suka gabatar ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.
"Muna da masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a ƙasar nan. Dole ne mu kawo ƙarshensu. Ku jami'an tsaro kun fi fahimtar muhimmancin hakan fiye da fararen hula."
"Muna tsammanin cewa ta hanyar ƙoƙarinku, za mu samu isassun albarkatun ƙasa da muke buƙata domin tabbatar da cewa mun samu tattalin arziƙi wanda zai zauna da ƙafafunsa."
- Bola Tinubu
Shugaba Tinubu ya kuma ba ƴan tawagar tabbacin cewa gwamnatinsa za ta kammala aikin hedkwatar NDC da ke birnin tarayya Abuja.
Karanta wasu labaran kan Tinubu
- PDP ta shirya daukar Tinubu aiki a zaben 2027, gwamna ya fadi kuskuren gwamnatin Tinubu
- Kowa ya rasa: Tinubu ya dakatar da siyar da shinkafar N40,000 ga 'yan Najeriya
- Dattawan Kudu sun raba gari da Tinubu kan kalamansa, siyasarsa ta samu koma baya
An bayyana maƙiyan shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya bayyana haƙiƙanin maƙiyan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Dogarin na Sani Abacha ya bayyana cewa hadiman Tinubu su ne haƙiƙanin maƙiyansa saboda yadda suka bari aka gudanar da zanga-zanga a ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng