Gwamnati ta Sake Daukar Mataki kan Kamfanin Jiragen Saman Arik, Bayanai Sun Fito

Gwamnati ta Sake Daukar Mataki kan Kamfanin Jiragen Saman Arik, Bayanai Sun Fito

  • Festus Keyamo, ministan sufurin jiragen sama ya ba da umarnin janye dakatarwar da aka yiwa kamfanin jiragen saman Arik
  • Rahotanni sun bayyana cewa janye dakatarwar ta biyo bayan sasanta kamfanin Arik da Atlas da ministan ya yi a kwanan nan
  • A wata sanarwa da hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama ta kasa (NCAA) ta fitar, kamfanin Arik zai dawo bakin aiki a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta dage dakatarwar da aka yiwa kamfanin jiragen saman Arik. Wannan na zuwa ne sama da mako guda bayan dakatar da ayyukan jiragen kamfanin.

An ruwaito cewa Festus Keyamo, ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, ya ba da umarnin a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: abin da Ministan Tinubu ya fadawa Sanusi II da miyagu suka lalata cibiyar NCC

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya janye dakatarwar da aka yiwa Arik Air
Kamfanin Arik Air zai dawo bakin aiki bayan gwamnati ta janye dakatarwar da aka yi masa. Hoto: @ArikAirlineNg
Asali: UGC

Daraktan hulda da jama'a da kare kwastomomi a hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa (NCAA) Michael Achimugu ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sasanta rikicin Arik da Atlas

Sanarwar da Michael Achimugu ya fitar ta ce:

"Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo da shugaban hukumar NCAA, Kyaftin Chris Najomo sun yi nasarar sasanta rikicin da ke tsakanin kamfanin Arik Air da Atlas Petroleum.
"Da wannan sasancin, kamfanin Arik zai iya fara jigilar fasinjoji daga yau.
Babban fifikon ministan da hukumar NCAA shi ne tabbatar da aminci da kuma lafiyar zirga-zirgar jiragen sama ga dukkanin fasinjoji."

Me ya jawo aka dakatar da Arik?

Sanarwar ta ci gaba da cewa yanzu haka fasinjoji sun fara bibiyar shafin Arik domin neman gurbin tafiya a jirgin kamfanin.

A ranar 30 ga watan Yuli, hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya NAMA, ta ce ta dakatar da wasu jiragen sama na Arik Air bayan umarnin wata kotu, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Bayan zanga zanga, Abba ya dauko muhimman ayyuka 7 domin farfaɗo da Kano

Hukumar ta ce umarnin kotun ya shafi bashin dala miliyan 2.5 da ake zargin kamfanin Atlas na bin kamfanin jiragen Arik.

An hana shugaban Arik shiga ofis

A wani labarin, mun ruwaito cewa hatsaniya ta barke a hedikwatar kamfanin jirgin saman Arik da ke a filin tashi da saukar jiragen saman Murtala Muhammed na birnin Legas.

Shugaban jami'an tsaron kamfanin jirgin, D Tom-West, ya ce an bashi umurni daga sama kada ya bar shugaban kamfanin Arik Air, Cif Johnson Arumemi-Ikhide ya shiga cikin harabar kamfanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.