Kamfanin sufurin jiragen sama na Arik sun sallami ma'aikatansu 300

Kamfanin sufurin jiragen sama na Arik sun sallami ma'aikatansu 300

- Arik Air, wani kamfanin sufurin jiragen sama a Nigeria, ya sanar da sallamar ma'aikatansa har 300 rigis

- A cewar kamfanin, sallamar mutanen ta zama dole ne saboda karyewar tattalin arzikin da suka fuskanta saboda ballewar annobar korona

- Bullar annobar korona ta haifar da dakatar da zirga-zirgar jama'a a ciki da wajen kasa domin dakile yaduwar kwayar cutar korono

Kamfanin sufurin jiragen sama na Arik Air a ranar Laraba ya sanar da zabge ma'aikata 300 inda suka bayyana cewa basa buƙatarsu, sakamakon karayar tattalin arziƙi da ta samu kamfanonin sufurin jiragen sama sanadiyyar ɓarkewar annobar COVID-19.

A cewar manajan hulɗa da jama'a da bayanai na Arik Air, Adebanji Ola, an ɗauki wannan matakin ne a ƙoƙarin da kamfanin ya ke don murmurewa tare da farfaɗowa don dawowa fagen fama da cigaba da ayyukan sufurin sama, kammar yadda The Nation ta wallafa.

Sannan ga haraji mai ɗumbin yawa wanda ya ke haddasa tsadar aikinsu a halin da ake ciki yanzu.

Kamfanin sufurin jiragen sama na Arik sun sallami ma'aikatansu 300
Kamfanin sufurin jiragen sama na Arik sun sallami ma'aikatansu 300 @Premiumtimes
Asali: Twitter

Ola ya ce shugabancin hukumar kamfanin ya zauna da ƙungiyoyin ma'aikata don ware wasu kuɗaɗen rage raɗaɗi da za'a biya korarrun ma'aikata.

Ya ce "ya na da muhimmanci a san cewar fiye da kaso 50% na kuɗaɗen da kamfani ya tara sun ƙare wajen biyan ma'aikata 1,600 haƙoƙinsu a watanni shidan da suka gabata."

"Shawarar sallamar ma'aikatan na da matuƙar wahala, amma ba yadda muka iya. Arik Air na yi wa sallamammun ma'aikatan kyakkyawan fata a rayuwarsu ta gaba."

A ranar Talata, 1 ga watan Disamba, 2020, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa shugaba Buhari ya bayar da umarnin sakin sabbin manyan motocin alfarma domin saukakawa jama'a kalubalen sufuri da rage musu radadin kara farashin man fetur.

Buhari ya mika sakon godiyarsa ga 'yan Najeriya bisa abin da ya kira 'hakurin da suka nuna' dangane da kalubalen tattalin arziki da kasa ke fuskanta

Kazalika, ya godewa mambobin kungiyar kwadago bisa fahimta da dattakon da kuma kishin kasa da suka nuna.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng