Izalah Ta Dauki Mataki kan Kuncin Rayuwa, Ta Turawa Limamai Sako Madadin Zanga Zanga
- Yayin da ake cigaba da zanga-zanga a Najeriya kan halin kunci, kungiyar Izalah ta sake tunatar da al'umma kan addu'o'i
- Shugaban kungiyar reshen Kaduna, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya sake kiran limamai a masallatai daban-daban sun dukufa addu'a
- Legit Hausa ta ji ta bakin wani limami kan wannan kira da Sheikh Bala Lau ya yi game da Alkunut a fadin Nigeria
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Shugaban Izalah reshen Kaduna, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya sake magana kan fara addu'o'i ga Najeriya.
Sheikh Bala Lau ya ce addu'o'in da za a yi sun hada da neman shiriyar shugabanni da sojoji da 'yan sanda da sauransu.
Zanga-zanga: Sheikh Bala Lau ya tura sako
Shehin malamin ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Laraba 8 ga watan Agustan 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina kira ga limamanmu, a cikin wannan kungiya muna da masallatan Juma'a sama da dubu 10 da na kamsul salawat sama da dubu 70."
"Duk wanda zai iya sauraron wannan kira daga gobe a sanya Alkunut da nufin Allah ya shiryar mana da shugabanninmu da sojojinmu da 'yan sanda."
"Ka ba su ikon tsayawa kan tsaro da kuma neman bunkasa tattalin arziki, wadanda suka addabe mu a daji suke tare hanya, Allah ka shiryar da su ida ba za su shiryu ba ka yi maganinsu."
"Duk masu ba su goyon baya a fili da na boye Allah ka yi mana maganinsu, muna rokonka Allah ka tausayawa Najeriya."
Zanga-zanga: Izalah ta yi addu'ar neman mafita
Bala Lau ya yi addu'ar Ubangiji ya dawo da tarbiya a cikin al'umma tsakanin dattawa da matasa da kuma yara.
Wannan kira na zuwa ne yayin da ake fama da tsadar rayuwa wanda ya tilasta mutane hawa tituna domin gudanar da zanga-zanga.
Jama'atul izalatul bid'ah wa ikamatus sunnah ba ta goyon bayan a fito ana yin zanga-zanga a titi.
Legit Hausa ta ji ta bakin wani limami kan wannan kira da Sheikh Bala Lau ya yi game da Alkunut.
Malam Muhammad Umar ya ce gaskiya mafi yawanci a masallatai ba a yin Alkunut kamar yadda aka buƙata.
Malamin ya ce duk da yanzu ayyuka sun yi masa yawa ba kasafai ya ke jan salla a masallacinsa ba amma ba a yin addu'ar sosai.
Sanusi II ya koka kan barna a zanga-zanga
Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya koka kan rawar da jami'an tsaro suka taka kafin faruwar zanga-zanga a jihar.
Sarkin ya ce tun kafin faruwar hakan an rubutawa jami'an tsaro domin daukar mataki amma suka yi sakaci har aka yi barna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng