Ministan Tinubu Ya Fadi Abin da Ya Dace 'Yan Najeriya Su Yi Maimakon Zanga Zanga

Ministan Tinubu Ya Fadi Abin da Ya Dace 'Yan Najeriya Su Yi Maimakon Zanga Zanga

  • Sanata Abubakar Kyari ya yi kira ga manoma a Najeriya da su mayar da hankali kan harkokin noma a ƙasar nan
  • Ministan na harkokin noma da samar da abinci ya buƙace su da mayar da hankali kan gonakinsu sannan su yi watsi da zanga-zangar da ake yi kan tsadar rayuwa
  • Ya bayyana cewa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta kawo shirye-shirye waɗanda za su bunƙasa harkokin noma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya yi kira ga manoman Najeriya da su mayar da hankali kan harkokin noma. 

Ministan ya yi wannan kiran ne yayin da yake magana kan zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan sabon halin ƙuncin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Betta Edu za ta koma kujerar minista? Tinubu ya yi muhimman sauye sauye a ma'aikatar jin ƙai

Abubakar Kyari ya ba 'yan Najeriya shawara
Abubakar Kyari ya bukaci 'yan Najeriya su daina zanga-zanga Hoto: @SenatorAKyari
Asali: Twitter

Ministan Tinubu ya shawarci ƴan Najeriya

Ministan ya ce yayin da farashin kayan abinci ya fara raguwa, dole ne a mayar da hankali wajen tabbatar da samar da abinci a ƙasar nan, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubakar Kyari ya yi kira ga ɗaukacin manoman Najeriya da su yi watsi da zanga-zangar adawa da gwamnati, maimakon haka su mayar da hankali kan gonakinsu.

Kyari ya yi kira ga manoma matasa da su mayar da hankalinsu da ƙarfinsu zuwa muhimman ayyukan noma domin a samar da abinci a ƙasar nan.

'Gwamnati na ƙoƙari' inji Abubakar Kyari

Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta ɓullo da manufofi da shirye-shirye ta hanyar ma’aikatar noma da samar da abinci domin bunƙasa harkokin noma.

Kyari ya ce tuni wadannan matakan suka fara haifar da ɗa mai ido yayin da farashin kayan abinci ya fara raguwa a fadin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Sojojin Najeriya sun yi magana kan kifar da gwamnatin Bola Tinubu

"Shugaba Tinubu ya kawo shirye-shirye masu muhimmanci da nufin tallafawa manoma a harkokin noma."

- Abubakar Kyari

Ministan ya ce zanga-zangar da ake yi za ta kawo koma baya ga ƙoƙarin samar da abinci da kawo cikas wajen safarar kayan abinci irinsu tumatir, wanda hakan zai jawo asara ga manoma.

Al-Mustapha ya faɗi maƙiyan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya bayyana haƙiƙanin maƙiyan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon dogarin na tsohon shugaban ƙasa Sani Abacha ya bayyana cewa hadiman Tinubu su ne haƙiƙanin maƙiyansa saboda yadda suka bari aka gudanar da zanga-zanga a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng