Ba a Mugun Sarki: Al Mustapha Ya Bayyana Hakikanin Makiyan Shugaba Tinubu

Ba a Mugun Sarki: Al Mustapha Ya Bayyana Hakikanin Makiyan Shugaba Tinubu

  • Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana hadimin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin maƙiyansa saboda ba su gaya masa halin da ƴan Najeriya ke ciki
  • Al-Mustapha ya caccaki jawabin da shugaban ƙasan ya yi saboda ya kasa biyan buƙatun da masu zanga-zangar ke nema
  • Tsohon dogarin na tsohon shugaban ƙasa Sani Abacha ya bayyana cewa sakacin hadiman Shugaba Tinubu ya sanya zanga-zangar ta rikiɗe ta zama rikici a wasu jihohin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya bayyana haƙiƙanin maƙiyan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon dogarin na tsohon shugaban ƙasa Sani Abacha ya bayyana cewa hadiman Tinubu su ne haƙiƙanin maƙiyansa saboda yadda suka bari aka gudanar da zanga-zanga a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Ana cikin zanga zanga, Tinubu ya aika sako mai ratsa zuciya ga 'yan Najeriya

Al-Mustapha ya fadi makiyan Tinubu
Manjo Hamza Al-Mustapha ya fadi makiyan Tinubu Hoto: Dr. Hamza Al-Mustapha, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Me Hamza Al-Mustapha ya ce kan Tinubu?

Al-Mustapha ya bayyana hakan ne yayin da yi watsi da kiran da wasu suke yi na sojoji su ƙwace mulki a ƙasar nan, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon sojan ya koka da cewa jawabin da Shugaba Tinubu ya yiwa ƴan Najeriya ya kasa biyan buƙatun da masu zanga-zangar ke nema.

Manjo Al- Mustapha ya caccaki Tinubu

Al-Mustapha, ya bayyana cewa sanar da lokacin fara zanga-zanga da masu shirya ta suka yi, ya isa ya ba shugaban ƙasa isashshen lokacin da zai hana a gudanar da ita, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

"Bana goyon bayan yin zanga-zanga. Na yi magana kan hakan sati uku da suka gabata. Na yi gargaɗi cewa kada a bari a gudanar da zanga-zangar."
"Abu mafi kyau shi ne masu zanga-zangar sun ba da sanarwa. Amma duk da sanarwar da suka ba da babu abin da aka yi kuma an fara gudanar da ita."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta dauki sabon mataki kan sanata Ali Ndume

"Hakan ya nuna cewa waɗanda ke kusa da shugaban ƙasan da suka bari zanga-zangar ta auku sun gaza wajen gudanar da ayyukansu."
"Tabbas akwai sakaci a tattare da su. Ba su goyon bayan shugaban ƙasan, da har suka bari ya karanta wannan jawabin."

- Manjo Hamza Al-Mustapha

Karanta wasu labaran kan Al-Mustapha

Tinubu ya roƙi ƴan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara kai zuciya nesa da gwamnatinsa.

Shugaban ƙasan ya ba da tabbacin ƙasar nan tana samun tagamoshi inda ta fara samun ci gaba maimakon koma bayan da ta samu a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng