Zanga Zanga: Aminu Ado Bayero Ya Sha Ruwan Yabo a Kano, an Bukaci a Yi Koyi da Shi

Zanga Zanga: Aminu Ado Bayero Ya Sha Ruwan Yabo a Kano, an Bukaci a Yi Koyi da Shi

  • Wata kungiya a jihar Kano ta kora yabo ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero kan rawar da ya taka wurin samar da zaman lafiya
  • Kungiyar Kano Progressive Movement ta ce Aminu Ado ya yi kokari musamman lokacin zanga-zanga domin a zauna lafiya
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake zanga-zanga a Najeriya kan tsadar rayuwa wanda aka shiga rana ta bakwai a fadin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - An yabawa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero kan rawar da ya taka yayin zanga-zanga a jihar Kano.

Kungiyar Kano Progressive Movement (KPM) ita ta kora yabon ga Aminu Ado inda ta ce ya yi rawar gani matuka.

Kara karanta wannan

Ana daga tutar Rasha, Amurka da Birtaniya sun fadi matsaya kan manufofin Tinubu

Aminu Ado ya samu yabo daga al'umma kan rawar da ya taka yayin zanga-zanga a Kano
Kungiya a Kano ta yabawa Aminu Ado Bayero kan taka rawar tabbatar da zaman lafiya yayin zanga-zanga. Hoto: @Engr_Alkasimfge, @mobilisingniger.
Asali: Twitter

Zanga-zanga: An yabawa Aminu Ado a Kano

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Legit ta samu wanda Alhaji Lawal Mohammed ya sanyawa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta ce basaraken ya tabbatar da zamna lafiya a tsakanin al'umma tare da dakile karuwar rikicin a sauran yankuna.

Lawal Mohammed ya ce sun yi imanin cewa hobbasan da Aminu Ado ya yi ya tabbatar da rawar da sarakunan gargajiya za su taka a cikin al'umma.

Hobbasan Aminu Ado a zanga-zanga

"Mun tabbatar da cewa abin da Aminu Ado ya yi ya nuna irin rawar da sarakuna za su taka wurin samar da zaman lafiya a cikin al'umma."
"Abin burgewa ne yadda basaraken ya ke kokarin tabbatar da zaman lafiya kuma kimarsa ta kara hada kan al'ummar jihar Kano."
"Muna yabawa tsari da halayen sarkin wanda ya kara masa kima da soyayya a tsakanin al'umma, shugabancinsa abin koyi ne ga duka 'yan Najeriya."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: A karshe, Ganduje ya yi magana, ya tura sako ga 'yan Najeriya

- Lawal Mohammed

Dan uwan Aminu Ado ya bi Sanusi II

Kun ji cewa yayin da ake cigaba da zanga-zanga a fadin Najeriya, Sarki Muhammadu Sanusi II na karbar baki a fadarsa da ke Kano.

Wasu daga cikin na hannun daman Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero sun kai ziyara fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.