“Abin da Ya sa Tinubu bai dawo da Tallafin Mai ba”: Minista ga Masu Zanga Zanga

“Abin da Ya sa Tinubu bai dawo da Tallafin Mai ba”: Minista ga Masu Zanga Zanga

  • Yayin da masu zanga-zanga ke neman dawo da tallafin mai, Wale Edun ya warware matsalar da ake fuskanta
  • Ministan kudi ya ce lokacin cigaba da biyan tallafi ya wuce a kasar kuma ba za a koma baya ba tun da an wuce wurin
  • Edun ya ce ba zai yiwu a dawo da tallafin man fetur ba saboda kwata-kwata babu shi cikin tsarin kasafin kudi na 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan kudi a Najeriya, Wale Edun ya yi magana kan dalilin da ya sa Bola Tinubu ba zai dawo da tallafin mai ba.

Wale Edun ya ce babu kason tallafin mai a cikin kasafin da Tinubu ya mika a Majalisar Tarayya na wannan shekara ta 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta sake magana kan dawo da tallafin man fetur da kawo saukin abinci

Minista ya yi karin haske kan dalilin da yasa Tinubu ba zai dawo da tallafi ba
Ministan kudi, Wale Edun ya yi magana kan dawo da tallafin mai. Hoto: @FinMinNigeria, @officialABAT.
Asali: Twitter

Zanga-zanga: Ministan Tinubu ya magantu kan tallafi

Ministan ya bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na AIT a jiya Talata 6 ga watan Agustan 2024 da muke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wale Edun ya ce Tinubu ya kawo gyara mai muhimmanci kan barnar da ake yi game da kudin da ake samu na tallafin.

Ya bayyana tsare-tsaren Tinubu na gaggawa da masu dogon zango domin rage farashin kaya musamman na abinci a kasuwanni.

"Babu maganar dawo da tallafi"- Ministan kudi

Har ila yau, Ministan ya ce kowa ya cire ransa saboda maganar dawo da tallafin mai ba zai yi wu ba kuma ya wuce kenan.

Wannan martani na Edun na zuwa ne bayan masu zanga-zanga sun yi korafi kan shugaban ya dawo da tallafin mai domin samun saukin rayuwa.

Shugaban kasar ya yi fatali da maganar dawo da tallafin mai a jawabinsa da ya yi a karshen mako.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi ya fadawa Tinubu hanyar dawo da tallafin mai cikin sauki

Zanga-zanga: Hafsoshin tsaro sun gana

Kun ji cewa Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya gana da shugabanin hukumomin tsaron kasar game da zanga-zanga.

Janar Musa ya dauki matakin ne bayan umarnin Bola Tinubu kan masu daga tutocin kasar Rasha yayin zanga-zanga.

Duk da ba a bayyana musabbabin ganwar ba amma hakan bai rasa alaka da umarnin da Bola Tinubu ya ba su a jiya Litinin 5 ga watan Agustan 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.