Kano: Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Amince da Fitar da N2.67bn domin Manyan Ayyuka

Kano: Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Amince da Fitar da N2.67bn domin Manyan Ayyuka

Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf a Kano ta amince da fitar da N268,160,455.84 domin samar da wasu manyan ayyuka a fadin jihar.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Majalisar zartarwar jihar ce ta amince da fitar da kudin bayan zamanta na ranar Talata, inda za a yi wasu ayyukan tituna da gyara ma'aikatar gwamnati.

Daga cikin ayyukan da gwamnatin za ta yi akwai samawa ma'aikatar sufuri ta jihar da masu ba wa gwamna Abba Kabir Yusuf shawara ofis.

Abba Kabir
Gwamnatin Kano za sake gina shataletalen da ta rushe Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A sanarwar da daraktan yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa ana sa ran ayyukan za su farfado da rayuwar jama'a.

Kara karanta wannan

Bayan zanga zanga, Abba ya dauko muhimman ayyuka 7 domin farfaɗo da Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Wasu manyan ayyukan da za a yi

1. Sake gina shataletalen gidan gwamnati

Daya daga cikin rusau da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi bayan kama mulki shi ne na shataletalen gidan gwamnati da aka gina a zamanin Abdullahi Umar Ganduje.

A wannan lokaci, an amince da fitar da ₦164,949,693.46 domin sake gina shataletalen a gadar Rabi'u Musa Kwankwaso da ke titin gidan sarki.

2. Samawa ma'aikatar sufuri gurbi

Majalisar zartarwa ta amince da fitar da ₦268,160,455.84 domin gyara wani sashe na babban dakin karatu na jihar.

Za a mayar da sashen da za a gyara ma'aikatar sufuri da ofisoshin masu ba wa gwamna shawara a kan al'amura da dama.

3. Gina cibiyar fasahar zamani

Wani gagarumin aiki da aka dauko shi ne gina cibiyar gwaji da na'ura mai kwakwalwa da fasahar zamani a kan kudi ₦309,784,126.72.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Majalisar matasan Arewa ta yi fatali da neman dauke cibiyar NCC daga Kano

Nigerian Tribune ta wallafa cewa ana sa ran cibiyar za ta bunkasa ilimin na'ura mai kwakwalwa da saukaka jarrabawa ta na'urar a Kano.

4. Gyara da gina tituna a Kano

Majalisar ta amince a kashe ₦77,540,743.19 domin gina kwalbati a hanyar titin Gwarzo-Shanono, sai ₦43,382,210.10 na gyaran titi mai tsawon kilomita biyu daga Riga zuwa Karkari a karamar hukumar Gwarzo.

An fitar da ₦30,579,961.24 domin gyara wurin kwanan dalibai mata a jami'ar Aliko Dangote da ke Wudil, sai kuma fadada titin gadar asibitin AKTH a kan ₦275,992,011.92.

Gwamnan Kano ya kaddamar da babban aiki

A baya kun ji labarin cewa gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin fara biyan hakkokin tsofaffin ma'aikatan jihar da aka shafe akalla shekaru uku ba a biya su ba.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya kaddamar da aikin, inda ya koka a kan yadda gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta gurgunta harkar biyan tsofaffin ma'aikata hakkokinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.