Zanga Zanga: Majalisar Matasan Arewa Ta Yi Fatali da Neman Dauke Cibiyar NCC daga Kano

Zanga Zanga: Majalisar Matasan Arewa Ta Yi Fatali da Neman Dauke Cibiyar NCC daga Kano

  • Bayan masu zanga-zanga sun farfasa sabuwar cibiyar hukumar sadarwa ta kasa a Kano, an fara samun kiraye-kirayen sauya masa matsuguni
  • Wasu mutane sun fara kokarin cusawa gwamnatin tarayya bukatar a mayar da cibiyar da aka kashewa makudan kudi gabanin lalata ta jihar Kebbi
  • Amma kungiyar Majalisar Matasan Arewa ta ce kiran bai dace ba, yayin da ta bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta gaggauta gyara cibiyar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Majalisar Matasan Arewa ya yi tir da bukatar da wasu mutane ke yi na gwamnati ta sauyawa cibiyar fasaha ta hukumar sadarwa (NCC) matsuguni.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe budurwa mai shirin zama amarya da wasu matasa a zanga zanga a Arewa

Kiran na zuwa ne bayan fusatattun matasan kasar nan sun lalata dukkanin kayan miliyoyin Naira da aka zuba a ciki da zummar habaka bangaren fasahar zamani a yankin Arewa maso Yamma.

Jihar
Majalisar Matasan Arewa sun ki amincewa da sauyawa cibiyar NCC wuri daga Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa a sanarwar da shugaban majalisar, Dr. Aliyu Mohammed da sakatarensa, Hafiz Garba su ka sanyawa hannu, sun ce bai kamata wasu yi rika irin wannan kira ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kano na da muhimmanci a Arewa," Matasa

Majalisar matasan Arewa ta ce duk da jihar Kebbi na bukatar manyan ayyukan ci gaba, amma jihar Kano na da muhimmanci wurin ci gaban Arewacin kasar nan.

Dr. Aliyu Mohammed, shugaban majalisar na ganin bai kamata a dauke cibiyar hukumar sadarwa ta kasa daga Kano ba, The Sun ta wallafa.

Matasa sun nemi gyara cibiyar NCC a Kano

Kara karanta wannan

An ga bidiyo ta koma talla, jama'a sun kawowa tsohuwar malamar makaranta tallafi

Majalisar matasan Arewa ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta bayar da umarnin gyara cibiyar NCC da aka lalata a Kano.

Matasa masu zanga-zanga sun fasa cibiyar da aka kammala gabanin kaddamar da ita, tare da yashe kujera da sauran na'urorin da aka sanya a ciki.

Kano: Matasa sun lalata cibiyar NCC

A baya mun ruwaito yadda matasa masu zanga-zanga su ka barnatar da dukiyoyin miliyoyin Naira a jihar Kano a ranar farko na fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu.

Matasan sun kutsa sabuwar cibiyar da ba a bude ba ta Digital Industrial Park inda su ka lalata kayayyakin da ke ciki, sannan sun wawashe wasu daga cikin kayan amfani da aka sanya a ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.