Yadda Aka Kashe Budurwa Mai Shirin Zama Amarya da Wasu Matasa a Zanga Zanga a Arewa
Zanga-zanga a Najeriya ta fara daukar sabon salo bayan an fara zargin jami'an tsaro da budewa jama'a wuta, tare da hallaka wasu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Daga cikin matasa akalla guda biyar da iyalansu su ka tabbatar da rasuwarsu ta hanyar harbi yayin zanga-zanga, hudu daga cikinsu masu karancin shekaru ne.
Zanga-zangar lumana ta tayar ta tayar da hazo bayan an samu wasu matasan na fashe-fashe, wasu jami'an tsaro kuma na harbin jama'a.
Daily Trust ta tattaro mutane akalla biyar ne su ka rasa rayukansu a jihohin Kano da Kaduna, a cikinsu har da wadanda harsashi su ka same sua gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin matasan da aka kashe a zanga-zanga
Da yawa daga cikin matasan da aka samu labarin rasuwarsu sun fito daga Kurna da Rijiyar Lemo da Kofar Nassarawa a jihar Kano.
Wasu daga cikin matasan sun hada da;
1. Firdausi mai shirin amarcewa
An samu rahoton rasuwar Firdausi Muhammad a unguwar Rijiyar Lemo a Kano, inda aka samu arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar lumana ranar Asabar.
'Yan uwan Firdausi sun ce harsashi ya tsallako har cikin gidansu ya same ta ana tsaka da shirin bikinta mako mai zuwa.
2. An kashe Umar a Kano
Matashi Umar Abubakar Hausawa ya rasu ranar Asabar a Kofar Nassarawa da ke jihar Kano, inda harsashin yan sanda ya same shi.
Dan uwan marigayin ya ce Umar ya fusata ne bayan wasu daga cikin kannensa sun fita zanga-zanga, kuma ya fita kiransu ne ajali ya riske shi.
3. Abdul-Kadir ya mutu a hanyar wajen sana'a
Matashi AbdulKadir Labaran Babah Alfindiki ya rasu a Kofar Nassarawa bayan ya shaidawa mahaifiyarsa cewa zai tafi wajen sana'arsa.
Mahaifiyar, Aisha Isah Babah ta ce ta shiga damuwa bayan danta ya ki dawo wa ya ci abincin rana, ashe ajalinsa ne ya cimma masa.
4. An kashe yaro dan shekara 15
Mahaifiyar matashi mai shekaru 15, Kashifu Abdullahi Gyaranya ta bayyana cewa danta ya ce zai fita ganin abokansa.
Maryam Sani ta ce sai da ta ja kunnensa kar ya karasa inda ake zanga-zanga, kuma ya ce ba zai je ba, daga bisani aka sanar da ita rasuwarsa.
5. An kashe mai shekaru 18 har gida
An yi zargin wani jami'in soja da harbe matashi Isma’il Muhammad har lahira a gidansu da ke Samuru a Zaria, Kaduna, Peoples Gazette ta wallafa.
Mahaifiyar marigayin, Zainab Sani ta ce yaron na wasa da 'yan uwansa lokacin da wani soja ya ka taho kansu, kuma har ya harbe shi.
An caccaki shawarar Atiku kan harbin jama'a
A baya mun ruwaito yadda gwamnatin tarayya ta ga rashin dacewar shawarar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ba jami'an tsaro.
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce jami'an tsaro sun yi kokarin wanzar da doka bayan masu zanga-zanga sun rikide zuwa kokarin tayar da hankulan jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng