Daga ba Jami'an Tsaro Shawara, Shugaban Kasa Tinubu Ya Caccaki Atiku Abubakar

Daga ba Jami'an Tsaro Shawara, Shugaban Kasa Tinubu Ya Caccaki Atiku Abubakar

  • Gwamnatin Najeriya ta zargi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da goyon bayan tashe-tashen hankula a kasar
  • Wannan ya biyo bayan shawarar da Atiku Abubakar ya ba wa jami'an tsaron kasar nan a kan harbin masu zanga-zangar lumana
  • An samu rahotannin harbin wasu 'yan Najeriya yayin gudanar da zanga-zanga wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mata, yara da matasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi martani ga tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar bayan shawartar jami'an tsaro da su daina harbin jama'a.

An samu rahotannin asarar rayukan matasa da yaran kasar nan da dama, musamman a jihohin Kano da Kaduna bayan sun yi kicibis da jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da manyan hafsoshin tsaro ana tsaka da zanga zanga

Atiku
Gwamnatin tarayya ta yiwa Atiku kan shawararsa ga jami'an tsaro Hoto: Atiku Abubakar/Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A sanarwar da mashawarcin shugaban kasa a kan yada labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya zargi Atiku Abubakar da goyon bayan tayar da hankula.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Jami'anmu sun nuna kwarewa," Onanuga ga Atiku

Mai ba wa shugaban kasa, Bola Tinubu shawara a kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya ce jami'an tsaron kasar nan sun nuna kwarewar aiki.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Onanuga ya ce duk da zanga-zangar lumana ta koma tashin hankali, jami'an tsaro sun yi iya kokarinsu.

Onanuga ya shawarci Atiku kan dattako

Bayo Onanuga ya shawarci Atiku Abubakar ya zama mai kishin kasa da nuna dattako ba tare da sanya son rai ko bambancin akidar siyasa ba.

Onanuga, wanda mashawarcin shugaba Tinubu ne ya ce abin da Atiku ya kamata ya yi shi ne jan kunnen jama'ar da ke ta'asa a jihohi da sunan zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Fargabar wawaso: An dauki mutum 800 domin tsare kasuwar Kano daga masu zanga zanga

Atiku ya karfafi masu zanga-zanga

A wani labarin kun ji yadda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yabawa matasan kasar nan da su ka fito tituna domin adawa da matsin rayuwa.

Ya shawarci matasan su ci gaba da nuna kuncin da su ke ciki ga mahukunta, yayin da ya yi kira ga shugaban kasa, Bola Tinubu ya gaggauta daukar mataki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.