Bidiyo: Bayanai Sun Fito da Soja Ya Harbe 'Dan Shekara 16 har Lahira a Garin Zariya
- Sojoji sun tafka barna a layin Sarkin Pawa da ke Samarun Zariya a jihar Kaduna bayan da wani soja ya harbe karamin yaro har lahira
- An ruwaito cewa sojojin sun bude wuta kan mai wuya da wabi a lokacin da suka shiga unguwar, inda kowa ya yi ta kansa, yaron ya shiga gida
- 'Yan uwan mamacin sun ce yaron na cikin gida lokacin da wani soja ya harbi kofar gidan har sau biyu inda ya sami yaron a makogoro
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zariya, Kaduna - Wani soja daga cikin jami'an tsaron da ke tabbatar da dokar hana fita a layin Sarkin Pawa da ke Samaru, Zariya, jihar Kaduna ya harbe yaro dan shekara 16.
An ruwaito cewa yaron mai suna Ismail Muhammad na wasa da abokansa a kofar gida lokacin da sojojin suka isa unguwar tare da tarwatsa kowa, inda yaron ya shige gida.
Soja ya kashe karamin yaro a Kaduna
Kamar yadda wani bidiyo da Saidu Shehu ya wallafa a shafinsa na Facebook, wani daga cikin yayyen yaron wanda ba a bayyana sunansa ba, ya ce an harbi yaron a makogoro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar dan uwan yaron da aka kashe:
"Muna waje sai aka ce ga sojoji nan suna raka mutane gida, sai muka shiga gida gaba daya, ni na rufe kofar da kaina, amma wani soja ya yi harbi ta kofar gidan ya samu kanina.
"Sun harbe shi a makogoro ne, kuma yana a cikin gida ba wai a waje ba. Yaron shekarunsa 16. Mun dauki gawar mun kai masu, suka yo kanmu da mota suna harbi."
Kalli bidiyon a kasa:
Sojoji sun hana jana'izar yaron
A wani faifan bidiyo na daban da @haidaer ya wallafa a shafinsa na X, an ga gawar yaron da aka kanshe kwance gaban motar sojoji, inda 'yan uwansa ke yiwa sojojin magana.
Wata majiya ta bayyana cewa 'yan uwan mamacin sun nemi sojojin su amince su sallaci gawar yaron amma suka ki yarda da cewar an sanya dokar hana fita don haka dole su koma gida.
Sai dai kuma, rahotanni sun bayyana cewa, daga bisani sojojin sun bar wajen, wanda ya ba jama'a damar yiwa yaron sutura bayan Sallar La'asar.
Kalli bidiyon a kasa:
'Yan uwan Ismail sun nuna takaicinsu
Mallam Muhammad, mahaifin Ismail da aka kashe, ya nuna takaicinsa kan yadda jami'an sojojin suka kashe masa dansa, kuma ya ce bai samu damar ganin gawar dan ba sai bayan awa daya da rabi.
Malam Kabir Muhammad Kasuwan Dare, Samarun Zaria ya yi kira ga jami'an soja da su yi adalci a bi wa marigayi Ismail Muhammad kadin jininsa da aka zubar.
"Saboda yin adalci ga iyayen Ismail da 'yan uwansa ne zai rage musu raɗaɗin rashinsa."
- A cewar Malam Kabir.
"Ayi adalci": Iyalan wanda aka kashe a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan uwan wani matashi Bashir Muhammad Lawan da jami'an tsaro suka kashe a Kano sun roki gwamnati ta bi kadin jinin dan uwansu.
Iyalan sun bayyana cewa an kashe dansu Bashir ne a lokacin da yake gudanar da zanga-zanga bisa ga 'yanci da dokar kasa ta bashi a matsayinsa na dan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng