Tsohon Gwamna a Arewa Na Daukar Nauyin Zanga Zanga? an Gano Gaskiya

Tsohon Gwamna a Arewa Na Daukar Nauyin Zanga Zanga? an Gano Gaskiya

  • Tun bayan fara zanga-zanga a Najeriya ake ta zarge-zarge kan wasu tsiraru da daukar nauyin matasan da ke hawa tituna
  • A wannan karon an juyo kan tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello inda ake zargin yana da hannu a zanga-zangar da ake yi
  • Sai dai Yahaya Bello ya yi kakkausar suka ga masu karya kan lamarin inda ya ce zai dauki matakin shari'a saboda bata masa suna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi martani kan jita-jitar da ake yadawa cewa yana daukar nauyin zanga-zanga.

Yahaya Bello ya musanta zargin da ake yi masa inda ya ce zai dauki matakin shari'a kan wadanda ke yadawa.

Kara karanta wannan

"Manyan Arewa da za su iya rarrashin masu zanga zanga," masoyin Tinubu ya fadi sunaye 2

Yahaya Bello ya yi martani kan daukar nauyin masu zanga-zanga
Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya musanta daukar nauyin masu zanga-zanga. Hoto: @OfficialGYBKogi.
Asali: Twitter

Yahaya Bello ya magantu kan zargin zanga-zanga

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Ohiare Michael ya fitar, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Michael ya ce suna kokarin daukar matakin shari'a kan dan gwagwarmaya, Jackson Ude da ya yada karairayin.

Ya ce wannan labarin ba shi da tushe bare makama kuma an yi ne domin bata sunan Yahaya Bello wanda yake kishin Najeriya, Daily Trust ta tattaro.

Zanga-zanga: Yahaya Bello zai shiga kotu

"Mun dauki wannan bayanai da labarin kanzon kurege, Yahaya Bello mutum ne mai kishin kasa wanda yake amfani da lokacinsa da arzikinsa wurin hada kan Najeriya."
"Muna kira ga 'yan sanda da hukumar DSS da sauransu da su yi bincike kan lamarin domin daukar muhimmin mataki."
"Wannan ba karamin al'amari ba ne saboda hakan barazana ne ga tsaron kasar Najeriya da al'ummar da ke cikinta."

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Yadda dan sanda ya bindige matashi a bainar jama'a, an shiga firgici

- Ohiare Michael

Wannan na zuwa ne bayan wani dan gwagwarmaya, Jackson Ude ya wallafa cewa tsohon gwamnan yana da hannu a daukar nauyin zanga-zanga.

Zanga-zanga: Hafsoshin tsaro sun shiga ganawa

Kun ji cewa Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa zai gana da shugabanin hukumomin tsaron kasar game da zanga-zanga.

Janar Musa ya dauki matakin ne bayan umarnin Bola Tinubu kan masu daga tutocin kasar Rasha yayin zanga-zanga da ake yi a fadin kasar baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.