"An Yi Abin Kunya", Rundunar Soja Ta Yi Tir da Masu Sata a Wuraren Ibada Ana Zanga Zanga

"An Yi Abin Kunya", Rundunar Soja Ta Yi Tir da Masu Sata a Wuraren Ibada Ana Zanga Zanga

  • Rundunar sojojin kasar nan ta magantu a kan yadda wasu masu zanga-zanga su ka lalata wuraren ibada na musulmi da kirista
  • Masu gudanar da zanga-zangar kukan yunwa da neman dauki daga gwamnatin Bola Tinubu sun yi sace-sace a masallatai da coci
  • An lalata wasu masallatai da coci a wasu jihohin da ke Arewacin kasar nan, har da Kano da Katsina wanda ya jawo abin suka

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Rundunar sojan Najeriya ta caccaki masu ɓuya a rigar zanga-zanga tare da lalata wuraren ibada a tattakin da ke gudana na kwanaki 10 a fadin kasa.

Kara karanta wannan

An kama matasa 632 a zanga zanga, kotu ta dauki matakin aika wasu zuwa kurkuku

Babban hafsan tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa ya bayyana takaicin irin ta'asar da aka tafka a wuraren ibada a cikin kwanaki shida na gudanar da zanga-zanga.

HQ Nigerian Army
Rundunar sojan Najeriya ta yi tir da lalata wuraren ibada lokacin zanga-zanga Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

.Jaridar Vanguard ta tattaro Janar Christopher Musa ya ce za su sanya kafar wanda daya da masu lalata wuraren ibada a jihohin Arewa , har da Kano, Kaduna da Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun barranta daga kiran masu zanga-zanga

Rundunar sojojin kasar nan ta jaddada matsayarta na jaddada mulkin dimokuradiyya a Najeriya duk da kiran da masu zanga-zanga ke yi.

Babban hafsan tsaro na kasa, Janar Christopher Musa ne ya jaddada haka, inda ya ce babban laifi ne daga tutar wata kasar da masu zanga-zanga ke yi.

Ya kara da cewa su na sanya idanu a kan yadda jami'an 'yan sanda ke magance matsalar da ta tunkaro kasar, kuma rundunar ba za ta nade hannu lamarin ya lalace ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun karbi mulki yayin da zanga zanga ta tsananta a Bangladesh, an samu bayanai

Tutar Rasha: An gargadi masu zanga-zanga

A baya mun ruwaito cewa rundunar sojojin kasar nan ta gargaɗi matasan da ke ɗaga tutar ƙasar Rasha yayin zanga-zanga da cewa hakan cin amanar ƙasa ne.

Babban hafsan tsaro na kasa, Christopher Musa ne ya yi gargaɗin bayan an gano gomman 'yan Najeriya su na daga tutar Rasha tare da neman ɗaukin Vladimir Putin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.