Karin Albashi: Gwamnatin Tinubu Ta Karo Kudin Shiga, Gwamna Ya Fadi Matsalar da Aka Fada

Karin Albashi: Gwamnatin Tinubu Ta Karo Kudin Shiga, Gwamna Ya Fadi Matsalar da Aka Fada

  • Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya koka kan yadda kayayyakin aikin yau da kullum suka tashi a kasuwannin Najeriya
  • Gwamnan ya ce tashin dala da karyewar Naira sun saka kudin da ake tura musu daga gwamnatin tarayya bai wadatarwa kamar da
  • Mutfwang ya yi magana ne bayan a ranar Lahadi shugaba Bola Tinubu ya ce yana turawa gwamnonin jihohi kudi fiye da shekarun baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya koka kan yadda kayayyaki suka yi tsada sosai a Najeriya.

Gwamna Caleb Mutfwang yana magana ne bayan shugaba Bola Tinubu ya karawa gwamnoni kudin shiga na wata wata.

Kara karanta wannan

"Garin kwaki ya fi karfin talaka": Tsohuwar shugabar NDDC ta tsagewa Tinubu gaskiya

Caleb Mutfwang
Gwamnan Filato ya koka kan tashin kayayyaki. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamna Caleb Mutfwang ya ce tashin farashin kayayyaki ya shafe su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Darajar kudi ya ragu' Inji Gwamna Mutfwang

Gwamnan jihar Filato ya bayyana cewa mutane suna iƙirarin cewa Bola Tinubu ya kara musu kuɗin shiga amma darajar kudin ta yi baya.

Gwamna Caleb Mutfwang ya ce idan aka duba abin da kudin za su iya saye za a ga maganar ƙarin ba ta da wani tasiri.

Saboda haka gwamna Caleb Mutfwang ya ce ya kamata mutane su rika kallon abin da za a kashe kudin dominsu ba kawai karin kudin ba.

Gwamnan Filato ya koka kan tashin dala

Rahoton Channels Television ya nuna cewa Mutfwang ya ce mutane da suke ta ruruta maganar ƙarin kuɗin ya kamata su duba farashin dala idan an kwatanta da Naira.

Caleb Mutfwang ya ce a idan aka lura a shekarar 2015 dala ba ta wuce Naira 180 ba amma a yanzu farashinta ya ninka sosai.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Tinubu ya dauki alkawari 1 yayin da ya fallasa shirin wasu 'yan siyasa

A kan haka ya nanata cewa farashin bakin mai, siminti da sauran kayan da suke ayyuka duk sun tashi ba kamar da ba kuma su suke laƙume kudin da ake tura musu..

Gwamna ya saka dokar hana fita a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da aka samu rikici, gwamnatin Plateau ta ɗauki matakin sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a wasu sassan jihar.

Gwamnan jihar, Mai girma Caleb Mutfwang ya sanya dokar a birnin Jos da Bukuru biyon bayan sace-sacen da wasu ɓata gari suka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng