An Gano Inda Masu Zanga Zanga ke Samun Tallafin Kudi, 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki

An Gano Inda Masu Zanga Zanga ke Samun Tallafin Kudi, 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce masu zanga-zanga na samun tallafin kudi daga waje, kuma tuni ta dauki matakin toshe wannan hanyar
  • Sufeta Janar na rundunar 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya bayyana hakan a taron manema labarai na jami'an tsaron kasar a birnin Abuja
  • A yayin da IG Egbetokun ya wanke 'yan sanda daga yin harbi da bindiga, rundunar sojin kasa ta ce za ta tabbatar da dimokuradiyyar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sufeta Janar na rundunar 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya sanar da cewa jami'an tsaro sun gano tare da toshe hanyoyin da masu zanga-zanga ke samun tallafi daga waje.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun ƙwace motar yaƙin ƴan sanda a Kaduna? Gaskiya ta fito

Kayode Egbetokun ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a ranar Talata, yayin taron manema labarai na jami'an tsaro.

Sufeta Janar na rundunar 'yan sanda ya yi magana kan zanga-zangar yunwa
'Yan sanda sun toshe hanyar da masu zanga-zanga ke samun tallafin kudi. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ne ya shirya taron a hedikwatar tsaro domin tattauna batutuwan da suka shafi zanga-zanga a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sufeta janar na rundunar 'yan sandan, jami'an tsaro sun yi taka tsan-tsan wajen magance matsalolin zanga-zangar.

'Yan sanda sun musanta yin harbi

Kayode Egbetokun ya ce ko kadan jami'an rundunar 'yan sanda ba su yi amfani da ruwan zafi ko harsashin roba kan masu zanga-zangar ba.

Shugaban ‘yan sandan ya bayyana cewa harbin da aka yi kan masu zanga-zanga a Kubwa, Abuja ba aikin jami’an tsaron nasu ba ne.

Ya yi nuni da cewa mai yiwuwa ‘yan fashi da makamai ko ‘yan bindiga ne suka yi harbin, inji rahoton Arise News.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan sanda na kokarin kakkabe miyagu, an kama 'yan daba 50 a Katsina

Sojoji za su tabbatar da dimokuradiyya

Babban hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa, ya jaddada kudirin hukumomin tsaro na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

“Ba za mu bari wani mutum ko kungiya su yi wa tsaron kasa da dimokaradiyyarmu zagon kasa ba. Muna aiki tukuru domin ganowa da hukunta masu hannu a tashin hankulan.

Dangane da batun tura sojoji, babban hafsan sojojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya tabbatar da cewa:

“Rundunar sojin Najeriya ta tsaya tsayin daka wajen goyon bayan dimokuradiyyar Najeriya, da zaman lafiya, da kwanciyar hankalin 'yan kasar.”

Kaduna: An kwace motar 'yan sanda?

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sanda ta yi martani kan rahotannin da ake yadawa a shafukan intanet na cewa masu zanga-zanga sun kwace motar 'yan sanda a Kaduna.

A cewar kakakin rundunar na kasa, Olumuyiwa Adejobi, masu zanga-zangar sun dare kan motar ne a lokacin da take kokarin barin inda ake zanga zangar kuma sun sauka kafin taje sansani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.