"Mun Tsaurara Matakan Tsaro,” Gwamnatin Kano ta Sassauta Dokar Hana Fita
- Gwamnatin Kano ta sassauta dokar hana fita ta awa 24 da ta sanya, inda a yanzu aka mayar da dokar daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma
- Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Salman Dogo ne ya sanar da hakan a ranar Talata bayan kammala taron majalisar tsaron jihar
- Kwamishinan 'yan sandan ya bukaci mazauna jihar da su ba jami'an tsaron da aka girke a ciki da wajen birnin Kano goyon baya da hadin kai
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnatin jihar Kano ta sake waiwayar dokar hana fita ta awa 24 da ta sanya a fadin jihar biyo bayan zanga-zangar yunwa da ta rikide zuwa tashin hankali.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Salman Dogo ne ya sanar da hakan a ranar Talata bayan kammala taron majalisar tsaron jihar da Gwamna Abba Yusuf ya jagoranta.
Gwamnatin jihar Kano ta ce dokar hana fita a jihar yanzu ta fara daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma, kamar yadda sanarwar mai tallafawa gwamnan, Hassan Sani Tukur ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kano: An sassauta dokar hana fita
Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa cikakkiyar sanarwar kwamishinan 'yan sanda a shafinsa na X, inda ya ruwaito Salman Dogo yana cewa:
"Gwamna Abba Yusuf, bayan tattaunawa mai zurfi da ‘yan majalisar tsaron jihar ya yanke shawarar sake sassauta dokar hana fita daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.
"An dai sassauta dokar hana fitar ne domin dawo da zaman lafiya a jihar, kuma jami’an tsaro za su kasance a dukkan sassan jihar domin tabbatar da doka da oda."
An tsaurara matakan tsaro a Kano
Kwamishinan 'yan sandan ya bukaci mazauna jihar da su ba jami'an tsaron da aka girke a ciki da wajen birnin Kano hadin kai domin dawo da zaman lafiya.
Ya kuma bukaci mazauna jihar da su rika komawa gidajensu a kan lokaci, inda ya ba su tabbacin cewa za a kara sassauta dokar gwargwadon tsaron da aka samu.
"Jami’an tsaro za su kasance a dukkan sassan jihar domin tabbatar da doka da oda, ana neman jama'a su ba jami'an hadin kai yayin gudanar da ayyukansu."
- A cewar kwamishinan.
Gwamnan Kano ya dauki matakai kan zanga-zanga
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Kano ta nuna takaicinta kan yadda wasu yan daba suka kwace zanga-zangar lumana suka mayar da ita ta ta'addanci a fadin jihar.
Domin magance matsalar zanga-zangar, Gwamna Abba Yusuf ya dauki matakai shida ciki har da bude cibiyoyin horar da matasa sana'o'in dogaro da kansu da kula da masu shaye-shaye.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng